Wasu dauke da bindigogi da ba a san ko su waye ba sun kai wa tsohon gwamnan jihar Akwa-Ibom sanata Godwill Akpabio hari da daren Talata inda aka yi ta ruwan alburusai tsakanin su da jami’an dake tsare sanatan.
Akpabio dai yana ganawar siyasa ce a gidan sa dake Ukana Ikot Ntuen, karamar hukumar Essien Udim, tare da wasu ‘yan siyasa a jihar.
Kakakin sanatan, Anietie Ekong ya bayyana a shafin sa na Facebook a daidai abin na faruwa cewa ” Ina sanar muku cewa wasu ‘yan bindiga sun kawo mana hari a gidan sanata a Akpabio. Har yanzu ana batakashi tsakanin maharan da jami’an tsaron da ke tare da sanata Akpabio.
” Kawai muna zazzaune fa sai muka ga mutanen da ke waje sun fado cikin dakin taron a guje. Kafin mu tambaye su ko me ke faruwa sai muka fara jin karan harbe-harben bindiga.” Inji Ekpong
Ekong ya kara da cewa a haka ne aka boye sanata Akpabio a cikin dakin taron da suke ganawar har sai da komai ya lafa.
Idan ba a manta ba, sanata Akpabio ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC a makonnin da suka gabata.
Hakan bai yi wa magoya bayan sa da yawa dadi ba da ya hada da gwamnan jihar.

Discussion about this post