Dalilan da ya sa dole Saraki ya sauka daga kujerar shugabancin Majalisa – Gbajabiamila

0

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila ya tattauna da PREMIUMTIMES, inda ya bayyana wasu dalilan da ya ce sun wajabta Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya sauka da shugabancin Majalisar Dattawa.

Bayan haka kuma Gbajabiamila ya amsa wasu tambayoyi da suka hada da sauya sheka da wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar sa a majalisa suka yi, kusanci sa da kakakin majalisa, da wasu batutuwa da dama.

PT: Na tabbatar da cewa ficewar mambobi 33 daga APC tilas ya girgiza ku. Kuma tabbas har yau jam’iyyar ku ba ta gama wartsakewa daga wannan wawakeken gibi da aka yi mata ba.

Gbajabiamila: To maganar gaskiya ai ficewar mamba daya tilo ma tilas ya girgiza mamba na majalisa daya, ballantana kuma a ce ficewar har mamba 33. Sai dai kuma daga baya mun koma mu na tausaya wa wadanda suka fice din, yayin da muka fahimci cewa ai sun tabka babban kuskure ne, wannan ficewar da suka yi.

Ai kuna gani, ba da dadewa ba kuma sai mu ka gane ashe ma ficewar ta su, kwallon mangwaro ne muka yada, kuma muka huta da kuda. Domin ficewar ta su ta kara nuna mana cewa ashe dai lallai jam’iyyar APC, jam’iyyar talakawa ce.

Rangadi da tarukan gangamin da aka yi bayan ficewar wadanda suka fice din ya nuna cewa mun yi wa APC mummunar fahimta a baya. A yanzu dai mun gane cewa jam’iyyar talakawa ce, ba ta rikakkun ‘yan siyasar da ke ji da kan su ba ce.

Sannan a yanzu talakawa sun gane masu kishin su da kuma masu kishin kan su. Don haka ina tabbatar maka cewa wadanda suka fice din nan, a yanzu da-na-sani kawai suke yi.

PT: Wasu na cewa abin da ya faru da APC, daidai ne, domin ita ma APC din haka ta yi wa PDP a cikin 2014, domin daga ficewar da aka rika yi ne a PDP ya sa har APC ta yi karfin da ta hau mulki. To me ya sa ku a yanzu ku ke jin haushin wadanda suka fice?

Gbajabiamila: Don wasu sun fice a zaben can baya, wannan ai ba dalili ba ne da zai sa a ce kowane zabe a rika samun masu tururuwar ficewa daga wannan jam’iyya zuwa waccan. Domin duk ana ficewa ne don kishin kai, ba kishin jama’a ko sauyin wata akidar siyasa ba.

Yawan ficewa daga jam’iyya zuwa waccan kada ya zama abin murna tunda ba da kyakkyawar akida ake ficewar ba. To idan ma ka ce an rama abin da aka yi a baya, to hakan ba dalili ba ne. Ya kamata ya kasance idan za aka fita, to ka fita akan wani dalili na akidar kishin jama’ar da suka zabe ka a karkashin jam’iyyar da suka zabe ka.

PT: Shin a halin yanzu ya karfin APC ya ke a Majalisar Tarayya? Har yanzu kuwa ita ke da rinjayen mambobi?

Gbajabiamila: Kwarai kuwa, har yanzu APC ce da mafi rinjaye. Domin ita ke da kusan 196, PDP kuma na da 150. Ka ga bambancin kusan 40 kenan. sannan kuma kada ka manta, wadanda suka koma ADC, su na da yakini, mu kuma mu na sa ran APC za su yi wa aiki, su na tare da APC a Majalisa.

Kuma ina tabbatar maka daga yanzu ba za ka kara jin an fice daga APC ba, sai dai an shigo APC daga wata jam’iyya.

PT: Da yawa na nuna damuwa da irin kalaman da ke fitowa daga bakin shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole a kan rikicin Saraki. Majalisa ta gindaya sharuddan da doka ta amince da su a bi wajen tsige shugaban majalisa, amma ya na nuna ko da tsiya sai an cire Saraki. Me za ka ce?

Gbajabiamila: Bari ka ji. Shugaban Jam’iyyar APC na magana ne fa a kan wajibcin dan adawa ya kasance shugaban majalisa, wanda bai yiwuwa wani ya rufe ido ya ce hakan daidai ne kasancewar dan adawa na shugabancin ta. To ni dai ban ga inda ma ka samo hujjar cewa Oshiomhole na kiran a cire Saraki a hanyar da ba ta dace ba.

PT: Shekaru hudu da suka gabata ka goyi bayan Aminu Tambuwal ya fice daga PDP ya koma APC, a lokacin ya na shubancin majalisa. Kai ne ma babban gogarma kuma Sarkin Yakin tabbatar da ba a tsige shi ba. Shin a yanzu ba za a rika kallon ka na nuna munafircin siyasa ba, da ka ke cewa sai Saraki ya sauka tunda ya fice daga APC?

Gbajabiamila: A wancan lokacin ai Majalisa ce gaba daya ta zabi Tambuwal. Kuma babu laifi mutum ya canja, idan ya na da dalili gamsasshe na doka da zai iya dogara da shi.

Iyalinmu da na Shugaban Majalisar Dattawa akwai kusanci sosai tun mu na yara. Don haka ba a lokacin siyasa na san Saraki ba. Dalili kenan maganar gaskiya ban so wannan rikici ya kazamce, har ya yi muni haka ba.

Idan da ni ne Shugaban Majalisar Dattawa, kuma ina a bangaren masu adawa a yanzu, shikenan sai na yi kutukutun da zan hana majalisa ta dawo ta zauna domin a zartas da amincewa da kudin da kasafin ayyuka?

Ko kuwa me ya hana shugaban majalisa dan bangaren adawa nada shugabannin kwamitocin da za su yi ayyukan tafiyar da sha’anonin ko ayyukan gwamnati?

PT: Amman kamar kawunan mambobin ku na APC a rarrabe ya ke a majalisar tarayya. Domin akwai ‘yan Kungiyar Gaba-dai-gaba-dai a karkashin Abdulmumin Jibrin. Ko akwai wani hubbasa da ku ke yi domin dinke wannan barakar?

Gbajabiamila: Kowa na da dama kafa kungiyar sa. Amma dai mu a majalisa da ke APC, kan mu a hade ya ke, uwar mu daya, uban mu ma daya.

PT: Me ke kusancin ka da Kakakin Majalisa, ganin cewa ka na hankoron hawa kan kujerar a zabe mai zuwa?

Gbajabiamila: Mu na zaman lafiya da shi, kuma mu na da kusanci, daram-dam mu ke. Har yanzu shi ne shugaba. Sannan kuma ban taba fitowa na ce ina neman kujerar sa ba. Ban kuma taba fitowa na ce ga abin da na ke so nan gaba ba. Saboda sanin gaibu sai Allah.

PT: An ce ka na fuskantar adawa mai karfi wajen kokarin ka na sake dawowa majalisa ka wakilci karamar hukumar Surulere a 2019. Shin ya abin ya ke ne?

Gbajabiamila: To sai ka nuna min dan majalisar da ba ya fuskantar adawa a mazabar sa. Hakan ai ba wani abu ba ne, siyasa ce. Kuma kowa ya san cewa zaben fidda gwanin jam’iyya shi ne alkali, kuma shi ne ‘yar manuniya mai nuna wanda jama’a suka fi karba hannu bibbiyu.

Share.

game da Author