Na dawo daga hutun kwana 10, zan ci gaba da ga inda na tsaya – Inji Buhari

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana wa manema Labarai a filin jirgin sama dake Abuja cewa zai hukunta duk wadanda aka kama na yi wa gwamnati zagon kasa a ayyukan ta.

A takarda da kakakin gwamnatin Buhari ya fitar Garba Shehu, ya ce tuni har shugaba Buhari ya aika wa majalisar Tarayya, da na dattawa domin sanar musu da dawowa daga hutu da kuma ci gaba da aikin sa na shugabancin Najeriya.

Buhari ya sauka a filin jirgin sama na Abuja da misalin karfe 6: 38 na yammacin Asabar.

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, sakataren gwamnatin Tarayya Boss Mustapha, Abba Kyari, da wasu gaggan gwamnati ne suka tarbi shugaba Buhari a Abuja.

Share.

game da Author