TSAKANIN BUHARI DA PDP: Kada fa hadama ya hadiye PDP a 2019, Daga Mohammed Mohammed

0

‘Yan Najeriya da dama na ganin cewa duk da matsin rayuwa da ake kuka da shi a kasar nan tun bayan rantsar da mulkin APC a 2015, Jam’iyyar PDP ba jam’iyyar da za a amince wa bane.

Sai dai kuma duk da haka da wasu ke fadi, da dama na ganin barusa, katobara, cin zarafin ‘yan Najeriya, tauye hakkin mutane ya fi zafafa fiye da zamanin mulkin PDP.

Gaba daya jam’iyyun da muke da su a kasa Najeriya, kowa ya zaro takobin sa ya wasa jira yake a buga gangar siyasa a fara sare-sare, munafunce-munafunce, don ganin an cimma abin da ake so.

Jam’iyyar PDP dai ta fi kowace jam’iyya fadawa cikin damuwa domin idan ba ta yi hankali ba hadamar ‘ya’yan jam’iyyar zai sa su kasa tabuka abin azo a gani ballantana tunkarar Buhari har suyi nasara.

Kusan duk wani jigo a jam’iyyar na so ya fito takarar shugabancin Najeriya, sannan babu wanda yake tunanin ya hakura ma daya.

Atikun ne ko Kwankwaso, ga Dankwambo, Makarfi, ga Tambuwal, Saraki, Tanimu Turaki, Datti Baba Ahmed, da dai sauran su.

Dukkan su na so su kada Buhari ne amma kuma shin daya zai yardan ma daya kuwa ko kuwa kasuwar ce za ta watsi daga karshe?

Zaben 2019, zabe ne tsakanin Buhari da PDP, domin kuwa cikin ‘yan siyasan da suka rage yanzu a APC, duk ba za su iya yi wa Buhari tasiri ba musamman a Arewa shine din dai shi kadai. Babban dalili kuwa shine wadanda ke da dan karfi a jihohin su duk sun ja daga da mutanen jihar su saboda haka suma ta kan su za suyi.

Akwai dai saurar rina a kaba ko PDP ta hakura ta yi abinda ya dace ko kuma su kwashi kashin su a hannu, hadama ya handame su.

Share.

game da Author