Sama da gidaje 50 ne suka lalace a sanadiyyar wata ambaliya ta yi barna a garin Dakingari, da ke cikin Karamar Hukumar Zuru a Jihar Kebbi.
Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ya ruwaito cewa an goce da ruwan can tsakar dare kamar yadda Babban Daraktan Hukumar Agajin Agajin Gaggawa ta Jihar ta bayyana, ta hannun Babban Sakataren ta, Rabiu Kamba.
Sai dai kuma ya kara da cewa duk da dimbin jama’a sun rasa gidajen su.
Ya ce tuni jami’an hukumar sa sun garzaya sun gano da idon su, domin buda takamaimen irin ta’adin da ambaliyar ta yi domin sanin irin matakin da za a dauka na gaggawa, musamman tallafa wa wadanda abin ya shafa.
Daga nan ya gargadi jama’a da su kaura ce wa amfani da ruwan rijiyar da ambaliyar ruwa ta shiga.