Wani magidanci mai suna Haruna Ali mai shekaru 35 ya kai karan mahaifin matar sa Adamu Mai-Takaima a kotun shari’a dake Magajin Gari a garin Kaduna da zargin sace masa mata.
Haruna ya bayyana a kotun cewa yau matar sa Hadiza Haruna ta yi watanni 11 a gidan mahaifin ta da sunan rashin lafiya sannan ta bar gidan sa batare da izinin sa ba.
” Ni dai ina rokon kotu da ta dawo mini da matata. Zan kula da lafiyar ta da kai na idan ma wai har bata da lafiya ne.
A nashi bayanan Mai- Takaima, wato mahaifin Hadiza ya ce tabas Hadiza bata da lafiya kuma tayi tsawon watanin 11 a gidan sa tana jinyar barin cikin da ta yi sau biyu.
Mai-Takaima ya kara da cewa a duk lokacin da Hadiza za ta baro gidan mijin ta Haruna zuwa gidansa sai ta nemi izinin mijin ta.
Bayan ya kammala duba sakamakon gwajin cutar da Hadiza take dauke da shi Alkalin kotun Musa Sa’ad ya yanke hukuncin canza wa Hadiza asibiti a duba cutar yoyon fitsari da take fama dashi don a warkar da ita.
Sannan shi kuma Haruna zai biya duk kudaden asibitin da ya kamata a biya.
Za a ci gaba da shari’ar ranar 11 ga watan Satumba.
Discussion about this post