• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    GANAWAR TINUBU DA NLC: Ƙungiyar Ƙwadago ta ce a tilas a soke ƙarin kuɗin mai, an shammaci ‘yan Najeriya

    Buhari-signing-2020-budget

    Gwamnatin tsohon shugaban kasa Buhari ta sanar da sabbin nade-nade a daidai ana rantsar da Tinubu shugaban kasa

    Minista Sadiya ta miƙa ragamar Ma’aikatar Harkokin Jinƙai ga Babban Sakatare

    2015-2023: ‘Na yi sukuwa ta lafiya, na kai zamiya lafiya’ – Buhari

    BANKWANA DA BUHARI: ‘Tinubu yau mafarkin ka ya zama gaskiya, Allah ya sa ka kai Najeriya fiye da inda na kai ta’ – Nasihar Buhari ga Asiwaju

    Tsakanin Sanata Barau da Gwamna Ganduje, Daga Jaafar Jaafar

    Ba zan jira Litinin ba, tun Lahadi zan mika mulki ga Abba Gida-Gida in kama gaba na – Ganduje

    RANTSAR DA TINUBU: Kotun Koli ta yi watsi da karar rashin cancantar Tinubu shiga zaɓen 2023

    RANAR RANTSAR DA TINUBU: Za mu hana makiyaya karakaina da shanu a cikin Abuja – Shugaban Miyetti Allah

    An Karrama gidan Jaridar PREMIUM TIMES da kyauta mafi daukaka a aikin Jarida na kasar Amurka

    BA DA MU BA, TAYA ƁERA ƁARI: PREMIUM TIMES ta nesanta kan ta daga ƙungiyar da ta jona sunan ta a shirya taron karrama wasu mutane

    KIRAN RUWA: ‘Ka wa Allah ka ɗaga mana kafa, kada ka kwace mana filayen mu har 9 da ka kunno kai a kan su – Makarfi ga El-Rufai

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

    QATAR 2022: Ko ƙasashen Afrika za su fidda nahiyar jin kunya a duniyar ‘yan ƙwallo

    DAGARGAZA ARGENTINA: Ƙasar Saudiyya ta ba da hutun kwana Ɗaya a wataya

    QATAR 2022: 2:1: Saudiyya ta kafa tarihin karya gadara da tutiyar buga wasan Agentina 36 a jere babu rashin nasara

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    Buhari ya tashi zuwa Saudiyya, zai yi Umra ta ƙarshe a matsayin sa na shugaban kasa

    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

    BIDIYO: NAJERIYA @62: Ra’ayoyin ‘yan Najeriya game da mulkin Buhari a tsawon shekaru 7 da suka gabata

    Buhari bai san ƴan ta’adda sun fidda bidiyon da suka ce sai sun sace shi da ni ba sai da na ziyarce shi – El-Rufai

    Dalilin da ya sa na raɗa wa wasu fitattun gine-gine, da titunan jihar Kaduna sunayen wasu fittattun ƴan asalin jihar

    HOTUNA: Ɗan Autan marigayi tsohon sarkin Kano Ado Bayero, Mustapha Ado Bayero, ya auri mata biyu ranar Asabar a  Kano

    BIDIYO: An yi wa ɗan takarar mu murɗiya a zaɓen fidda gwani na APC a Legas – Masu zanga-zanga

No Result
View All Result

Dabbobin Layyah Da Kwanaki Goman Farkon Zul-Hajj, Daga Imam Murtadha Gusau

Premium Times HausabyPremium Times Hausa
July 29, 2020
in Ra'ayi
0
Rams

Rams

Bismillahir Rahmanir Rahim

Bayan haka, yaku bayin Allah! Ku sani, daga cikin muhimman lokuta na yin ibada, masu falala, da Allah Madaukaki ya hore wa bayin sa, akwai kwanaki goma na farkon watan Zul-Hajj – wata na sha biyu na shekarar Musulunci, wadanda Allah Ya fifita su a kan sauran kwanakin shekara.

Ibn Abbas ya ruwaito cewa, Annabi (SAW) ya ce:

“Babu wani aiki da yafi alheri irin wanda aka yi a kwanaki goma na farkon Zul-Hajj.” Sai wadansu Sahabbai suka ce: “Koda jihadi a tafarkin Allah?” Annabi (SAW) ya ce: “Koda jihadi a tafarkin Allah, sai dai in mutum ya tafi da kansa da dukiyarsa bai dawo da komai ba.” [Buhari]

Wadannan kwanaki goma manya ne kuma mafiya soyuwa ne a wurin Allah. Ibn Umar (RA) ya ruwaito cewa, Annabi (SAW) ya ce:

“Babu wasu ranaku da suke da girma kuma suka fi soyuwa a wurin Allah fiye da wadannan kwanaki goma na farko Zul-Hajj, don haka ku yawaita tahlili da takbiri da tahmidi a cikinsu” [Musnad Imam Ahmad, kuma Sheikh Ahmad Shakir ya inganta shi]

Daga cikin darajojin da wadannan kwanaki goma suke da su akwai cewa:

1- Allah Yana yin rantsuwa da wani abu domin Ya nuna muhimmancinsa, kuma Allah Ya yi rantsuwa da wadannan ranaku goma a cikin Alkur’ani Mai girma inda ya ce:

“Ina rantsuwa da alfijiri. Da darare goma.” [Al-kur’ani, 89:1-2]

Malamai magabata da suka hada da Ibn Abbas (RA) sun ce wadannan darare goma da aka ambata a cikin Alkur’ani su ne darare goma na farkon Zul-Hajj.

2- Annabi (SAW) ya ce wadannan darare goma sune ranaku mafiya alheri na shekara, kamar yadda muka ambata a Hadisi na baya.

3- Su ne ranaku mafiya alheri na yawaita ambaton Allah, kamar yadda Hadisin da ya gabata ya nuna.

4- Sun kunshi ranar Arfa (9 ga Zul-Hajj) wanda a cikinta ne Allah Ya cika wannan addini. Kuma yin azumi a cikin wadannan ranaku yana kankare kananan zunuban shekarar da ta gabata da shekarar da ake ciki, (manyan zunubai suna bukatar tuba da mayar da hakki ga mai shi).

5- Sun kunshi ranar “Hajji Mafi girma” wato ranar Idin Layya (10 ga Zul-Hajj), kuma wannan rana ita ce rana mafi girma a daukacin shekara.

Don haka ku yawaita karatun Alkur’ani a cikinsu, kuyi sallolin nafilah da kiyamul Laili da sadaka da yada ilimi da tuba ga Allah. Ku yawaita neman gafara ta fadin Astagfirullah, kuyi azumi da jikinku, ma’ana ku kaurace wa haram ko fadin haram ko sauraren haram da sauransu. Kuma ku yawaita yin addu’o’in alheri da zaman lafiya ga kasar mu Najeriya, da al’ummar Musulmin Najeriya, da al’ummar Musulmin duniya baki daya.

Imam Murtada Gusau

Yaku ‘yan uwa na maza da mata! Lallai ku yi gaggawar ribatar wadannan ranaku kafin lokaci ya kure muku.

Yaku bayin Allah! Ku sani, a yau, babu wani aikin da yafi hada dukan Musulmi, matasa da dattawa, maza da mata, bakake da farare, kuma yake kawo farin ciki a fuskar kowa, kamar ibadar Layyah. Layyah ibada ce ta sadaukarwa, ta hanyar yanka dabbobi domin neman yardar Allah. Ana yin ta ne domin tunawa da wani muhimmin abin tarihi da ya auku a lokacin da Allah Ya umarci Sayyidina Ibrahim (AS) ya yi layyah da dansa Sayyidina Isma’il (AS). A lokacin da yake shirin aiwatar da umarnin Allah, sai Allah Ya musanya masa da rago, ya canji Annabi Isma’il da shi, wanda Sayyidina Ibrahim (AS) ya yanka.

Sayyidina Ibrahim (AS), ya ci jarrabawa, domin ya shirya don ya yanka dansa saboda bin umarnin Allah. Yaku Abokaina masu girma, yanzu kuna jin wahala ku yi layyah da dabba (ta amfani da kudinku) don bin umarnin Allah? Bai kamata ni da ku mu kasa cin wannan jarrabawa ba. duk wanda yake da hali yayi layyah, a madadin sa da iyalinsa.

’Yaku ‘yan uwana maza da mata! Ku sani, za’a iya yanka Layyah a kowane lokaci bayan Sallar Idi har zuwa faduwar rana ta uku a bayan ranar Idin. Wannan na nufin wuni hudu (wunin Idi da karin wuni uku na ayyamut-tashriq). Kamar yadda Imamu Shafi’i ya nuna. Amma a fahimtar sauran manyan malamai: Abu Hanifah da Malik da Ahmad, ana yin layyah ce a cikin wuni uku. A fara da ranar Idi a kare a wuni na biyu bayan wunin Idi lokacin faduwar rana.

Ana iya yanka Layyah da rana ko da dare, matukar dai a cikin wadannan ranaku ne, amma yin ta da wuri (jim kadan bayan Sallar Idi) ya fi.

Sunnar Layyah ita ce a raba naman uku, kuma ba tilas ba ne a raba daidai-wa-daida. daya a raba wa talakawa da mabukata, dayan a bar wa iyali da makwabta da dangi da abokai, dayan kuma ka yi yadda ka so da shi.

Layyah Sunnah ce mai karfi a kan kowane Musulmi mai hali. Wannan shi ne ra’ayin akasarin malamai. Amma a wurin wadansu malaman wajiba ce a kan Musulmin da yake da halin yi. Kuma tana daya daga cikin kyawawan ayyuka a Musulunci kamar yadda A’isha (RA) ta ruwaito daga Annabi (SAW) cewa:

“Dan Adam bai taba yin wani aiki a ranar Layyah da ya fi soyuwa a wurin Allah ba, kamar zubar da jinin dabba (yankan Layyah).”

Kuma galibin malamai sun tafi a kan cewa, yanka Layyah shi yafi alheri a kan yin sadaka da kwatankwacin kudin abin yankar.

Yaku ’yan uwana! Ku sani, ana yin Layyah ne da dabbobin gida wato: shanu da rakuma da tumaki da awaki. Kuma yanka rago/tunkiya da bunsuru/akuya shi yafi a kan sauran dabbobin, saboda Annabi (SAW) bai taba yin Layyah ba face da wadannan dabbobi. Amma ana iya yanka rakuma da shanu lokacin Layyah. Kuma wajibi ne abin yankan ya kasance lafiyayye, kosasshe da za’a iya cin naman sa a matsayin ibada ga Allah kamar yadda Allah Ya ce:

“Kuma wanda ya girmama ibadojin Allah, to lallai ne ita (girmamawar) tana daga ayyukan zukata na takawa.” [Al-kur’ani,22:32]

Don haka dabbobi marasa lafiya ko masu aibu basu yin layyah.

Kuma wajibi ne idan rago ne ko tunkiya su haura wata shida kamar yadda Ibn Majah ya ruwaito cewa, sai Jaza’a za’a yi Layyah da ita. Ga jinsin akuya kuwa wajibi ne ya kai shekara daya. Sannan saniya shekara biyu, shi kuma rakumi shekara biyar.

Kuma kada a yi Layyah da nakasasshiyar dabba, kamar mai ido daya ko marar lafiya ko gurguwa da hakan ya bayyana ko ramammiya marar nama kamar yadda Buhari ya ruwaito daga Barra’u Bin Azib daga Annabi (SAW).

Kuma mafi yawan malamai sun tafi a kan cewa siffofi hudu da aka ambata a Hadisin za’a iya amfani dasu wajen hukunci a kan duk wata nakasa. Don haka duk wata nakasa da ta kai ta ko tafi ta ba za’a yi Layyah da dabbar ba, kamar makauniya ko marar kafa daya.
Kuma ana iya Layyah da dabbar da aka dandake, saboda Annabi (SAW) ya yi haka. Haka dabbar da aka haifa ba ta da jela/bindi ko take da rabinta, amma wadda aka yanke jelarta/bindinta duka ba za’a yi Layyah da ita ba.

Sannan tunkiya ko akuya daya ta wadatar mai gida yayi Layyah da ita ga kansa da iyalansa. Kuma ya halatta mutum bakwai su yanka saniya ko rakumi daya a matsayin layyarsu. Kamar yadda Jabir Bin Abdullahi (RA) ya ruwaito cewa Annabi (SAW) ya yi haka a shekarar Sulhun Hudaibiyyah. [Muslim]

Kuma mai yin haka zai iya hadawa da iyalinsa a cikin ladan domin a nan daidai yake da mai yanka tunkiya ko akuya.

Kuma bai halatta a yanka Layyah kafin yin Sallar Idi ba, duk wanda ya yanka layyah kafin Idi ya yanka wa iyalinsa nama sun ci ne kawai amma bai yi Layyah ba, kamar yadda Annabi (SAW) ya nuna. Kuma idan mutum zai yanka layyar ya ambaci sunan Allah, ya ce:

“Bismillah, Ya Allah, wannan daga rahamarKa ce kuma dominKa ne.”

An fi so mutum ya yanka Layyarsa da kansa, idan ba zai iya yin haka ba, to ya halarci yankan, sannan ya raba naman uku kamar yadda muka ambata a baya. Ya ci rubu’i daya shi da iyalinsa, ya bayar da daya rub’in sadaka, dayan kuma ya yi kyauta da shi, kamar yadda Annabi (SAW) ya shaida wa ’yarsa Fatima (RA) cewa:

“Ki kasance a lokacin da ake yanka Layyarki. Allah Yana gafarta miki a lokacin digar farko na jininta.” [Baihaki da Abdul Razzak]

Hikimar shar’anta yin Layyah:

1 – Neman kusanci ga Allah ta hanyarta.

2 – Raya Sunnar Shugaban Masu Tauhidi Annabi Ibrahim (AS) wanda Allah Ya umarce shi yayi Layyah da dansa Annabi Isma’il (AS) sannan daga baya ya musanya shi da rago, Annabi Ibrahim (AS) ya yanka shi a madadin Annabi Isma’il (AS) din.

3 – Yalwatawa da kyautata wa iyali a ranar Idi.

4 – Fadada jin dadi a tsakanin matalauta da mabukata ta hanyar ba su sadakar naman Layyah.

5 – Yin godiya ga Allah kan yadda ya hore mana duka dabbobin ni’ima (Bahimatil An’am).

Abubuwan da wanda yayi niyyar Layyah zai guje musu:

Idan mutum yayi niyyar zai yi Layyah to da zarar watan Zul-Hajj ya kama, ba zai yi aski ko ya yanke farce/kumba/akaifa ba har sai ya yanka abin Layyarsa. Muslim ya ruwaito a cikin Sahihinsa cewa Ummu Salmah (RA) cewa, Annabi (SAW) yace:

“Idan kuka ga jinjirin watan Zul-Hajj kuma dayanku yana da niyyar yin Layyah, to kada ya aske gashinsa ko ya yanke farcensa.” [Muslim]

Haka kada a biya ladan mai gyara naman Layyah daga abin Layyar. Domin Aliyu Bin Abi Talib (RA) ya ce:

“Manzon Allah (SAW) ya umarce ni da in lura da Layyar wani rakumi, in bayar da namansa da fatarsa a matsayin sadaka, kuma kada in bayar da komai daga cikinta ga mahauci a matsayin ladan aikinsa. Ya ce, “Zan iya ba shi wani abu daga abin da na mallaka.” [Muslim]

Yaku ‘yan uwana maza da mata! Ina rokon Allah Madaukaki ya amsa min da kuma ku da sauran Musulmin duniya baki daya, kuma Yasa dominSa kadai muke yi. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Annabi Muhammad (SAW) da iyalansa da Sahabbansa. Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai.

Ya Allah! Ka taimake mu wajen rayuwa bisa koyarwar Alkur’ani da Sunnah. Ya Allah Ka nuna mana gaskiya kuma Ka bamu ikon bin ta, kuma Ka nuna mana karya Ka bamu ikon guje mata.

Ya Allah! Ka shiryar da mu, Ka kare mu daga ayyukan jahilci da barna. Ka kare mu daga gazawarmu. Ka sanya karshen ayyukanmu su kasance mafi alherinsu da dacewarsu. Kuma Ka gafarta mana Ya Ubangiji.

Yaku ’yan uwana! Ku sani, duk abin da na fada mai kyau a wannan jawabi na yau, daga Allah Madaukaki ne, kuma duk wani kuskure daga gare ni ne, kuma ina neman tsarin Allah daga bayar da muguwar shawara da dukkan barna da fitina. Kuma ina rokon Allah gafara idan na ketare iyaka a cikin duk abin da na ce ko na aikata.

Godiya ta tabbata ga Allah, Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Manzon Allah da alayensa da Sahabbansa.

Ina mai kammala wannan jawabi nawa, ina mai rokon Allah Madaukaki Ya gafarta mana zunubanmu. Ku nemi gafararSa, Lallai Shi Mai gafara ne Mai jin kai.

Imam Murtadha Muhammad Gusau, Babban Limamin Masallacin Juma’ah na Nagazi-Uvete, da Masallacin marigayi Alhaji Abdurrahman Okene, da suke Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za a iya tuntubar sa ta lambar tarho kamar haka: +2348038289761 ko email: gusaumurtada@gmail.

Tags: AbujaEidHausaKabirKiaymul LailLabaraiLayyahPREMIUM TIMESSallahZul-Hajj
Previous Post

An ceto mutane bakwai daga hannun mai safarar mutane a kan iyakar Katsina

Next Post

Ambaliya ta ci gidaje 50 a Kebbi – Jami’in gwamnati

Premium Times Hausa

Premium Times Hausa

Next Post
Flood

Ambaliya ta ci gidaje 50 a Kebbi – Jami’in gwamnati

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • SHARI’AR ZAƁEN SHUGABAN ƘASA: Tinubu da INEC sun ƙi amincewa da tulin kwafe takardun da Atiku ya kwafo daga iReV
  • GANAWAR TINUBU DA NLC: Ƙungiyar Ƙwadago ta ce a tilas a soke ƙarin kuɗin mai, an shammaci ‘yan Najeriya
  • HAJJI 2023: Gwamnatin Filato ta bar mahajjatan jihar su na hajijiya a Madina
  • Kada ku tausaya min don na faɗi zaɓen Sanatan Zamfara – Sanata Marafa
  • JIRAN TSAMMANI: Tinubu zai saka wa waɗanda su ka yi wa APC hidima da waɗanda su ka wahala saboda jam’iyya – Marafa

Abinda masu karatu ke fadi

  • auto verkopen on ZAMFARA: Mahara sun gudu sun bar bindigar harbo jiragen sama a dajin Gumi da Bukkuyum -Inji ‘Yan Sanda
  • Laser-Haarentfernung mit hygienischen Bedingungen und aktuellen Gesundheitsstandards in der Türkei on An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • Call Girls Sehore on Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali
  • buy aged stripe account on Hukumar NBC ta gayyaci mai gabatar da shirin ‘Berekete’, bayan macen da ta kona gashin kan yarinya barkatai, ta sha mari barkatai a hannun sa
  • research and survey on Gwamnan Edo ya bijire wa umarnin kotu, ya ce sai mai shaidar rigakafin korona zai yi sallar jam’i a masallaci

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.