Tambuwal yayi wa siyasa ganganci, sannan ga yaranta kuma – Inji Wammako

0

Tsohon gwamnan jihar Sokoto Aliyu Magatakarda Wammako, ya caccaki gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal cewa yaran ta ne ya kwashe shi ya sa ya fice daga APC zuwa PDP.

” Ina yabawa Tambuwal ganin sa matashi mai kwazo sannan yana da himma a siyasa, amma yayi gaggawar ficewa daga APC. Bai yi shawara ta gari ba. Kuma ina tabbatar maku da cewa sai yayyi da na sani.

” Da ya sani sannan ya na tare da mutanen jihar Sokoto da ba haka ba. Sadoda haka ina tabbatar muku da kuyi watsi da yawan mutanen da kuka gani a taron sa, duk bula ce. Jihar Sokoto ta Buhari ce kuma jihar APC ce.

Idan ba a manta ba jam’iyyar PDP ta Gwamnan jihar Sokoto, Tambuwal ya fice daga jam’iyyar APC zuwa PDP a farkon wannan mako a wani taron dubban magoya bayan sa a gidan gwamnati dake Sokoto.

Tambuwal ya ce gazawar gwamnatin Buhari da jam’iyyar APC ne ya sa ya fice daga jam’iyyar.

Share.

game da Author