Shugaban kungiyar kula da lafiya ta duniya (WHO) Wondimagegnehu Alemu ya yi gargadin cewa nan da shekaru 32 masu zuwa mutane miliyan 10 za su rasa rayukan su a duniya duk shekara idan ba a gaggauta daukar mataki kan yadda mutane ke kin bin umarnin likita wajen shan magani ba.
Kungiyar ta ce hakan na daga cikin matsalolin da kungiyar ke kira akai.
Alemu ya ce bisa ga binciken nasu mutane miliyan takwas daga cikin miliyan goma da za su iya rasa rayukan su za su fito daga kasashen Asia da Afrika ne sannan sauran daga kasashen duniya.
Bayanai sun nuna cewa mutanen Najeriya za su fi fadawa cikin wannan matsala.
” Binciken da muka gudanar a Najeriya ya nuna cewa fannin kiwon lafiyar kasar na fama da matsalolin baragurbin ma’aikata, jabun magunguna da rashin amfani da magani yadda aka umarci mara lafiya ya yi amfani da shi.
A karshe ya yi kira ga gwamnatocin duniya musamman Najeriya da su gaggauta daukan matakai don shawo kan wannan matsala kafin a yi da na sani.