Sakataren APC na Kasa, Bolaji Abdullahi, da ‘yan majalisar jihar Kwara sun koma PDP

0

Sakataren APC na Kasa, Bolaji Abdullahi, ya fice daga APC, sannan kuma ya ajiye mukamin sa a jam’iyyar mai mulki.

Abdullahi ya bayyana ficewa daga jam’iyyar a cikin shafin san a tiwita.

Abdullahi, wanda dan gaban goshin Saraki ne, ya ajiye mukamin na sa a ranar Talata, kuma ya fice daga jam’iyyar a yau Laraba.

Bayan haka kuma Kakakin majalisar dokokin jihar Kwara Ali yususf dukkan su gaba daya sun canza sheka daga APC zuwa PDP.

Share.

game da Author