USAID ta tallafa wa asibitoci 169 a jihar Kogi

0

Hukumar raya kasashe ta Kasar Amurka, USAID ta tallafawa cibiyoyin kiwon lafiya 169 a jihar Kogi da kayan aiki da ya kai miliyan 35.

Jami’in hukumar Alobo Gabriel ya sanar da haka a lokacin da yake raba wadannan kayan aikin wa asibitoci a garin Lokoja.

Ya ce sun zabi asibitocin da za su tallafa musu ne bisa ga yawan mutanen da asibitocin dake kula da su.

Sannan hukumar ta horar da ma’aikatan asibitocin 2000 domin inganta aiyukkan da suke yi.

USAID ta horas da ma’aikatan asibiti 2000 domin bunkasa aiyukkan da suke yi ta kowace fanni sannan a yanzu haka ta na horas da karin wasu ma’aikatan a jihar.

” Sannan mun tallafa musu da na’urori yin gwaje-gwaje, gadajen kwanciya dakunan haihuwa da dai sauran us.

A karshe kwamishinan kiwon lafiyar jihar Saka Audu ya jinjina wa hukumar sannan ya ce ” Wannan tallafi da muka samu zai taimaka wajen rage matsalar mutuwan mata da yara kanana da muke fama da su a jihar.”

Share.

game da Author