Kwamitin Zartaswar Jam’iyyar APC ya gudanar da wani taron gaggawa a jiya Talata inda ya fitar da wasu zarge-zarge a kan Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki.
APC ta zarge shi da yi wa jam’iyya zagon-kasa da sauran laifukan da suka karya dokar kundin tsarin jam’iyyar na 21.
Wannan Sashe na 21, ya na magana ne a kan yadda jam’iyya za ta ladabtar duk wani dan jam’iyyar da ya karya doka, ta hanyar, ‘‘Duk wasu ayyuka da suka tozarta jam’iyya ko suka haddasa mata tsana da kiyayya, muzantawa, zubar mata da martaba da sauran irin haka.”
APC ta yi wannan ganawa ne a tsakanin shugabannin ta sa’o’i kadan bayan Saraki ya yi sanarwar ficewar sa daga APC ya koma PDP.
A bayanin da ta zartas a wurin taron, Sakataren Jam’iyyar na Kasa, Mai Mala Buni, ya nemi Saraki ya amsa tuhumar da jam’iyyar keyi masa a cikin sa’o’I 48.
Ga Tuhume-Tuhumen
“Kai ne kanwa-uwar-gamin kulla kutunguilar ficewar Sanatoci daga jam’iyyar APC zuwa wasu jam’iyyun adawa.
“Kiri-kiri ka ki zaman tantance sunayen wasu da Shugaba Muhammadu Buhari ya nada a kan wasu mukamai, wadanda kuma ‘yan jam’iyyar APC ne. Wannan ya jefa APC cikin matukar jin kunya, kuma tozartawa ce ka yi wa gwamnatin APC.
“Ka je jihar ka, ka shirya gangami inda magoya bayan ka suka nemi ka fice daga APC ka koma PDP. Bayan wannan ganganmi da ka yi, sai shi kuma Gwamnan Jihar Kwara, wanda dama dan gaban goshin ka ne, shi ma ya fito ya yi sanarwar cewa wa’adin kwanakin sa cikin APC sun kusa cika. Wannan ya nuna cewa kun nuna ficewar za ku yi.
“Ka yi amfani da ofishin Shugaban Majalisar Dattawa ka haifar da tsaiko da jinkiri na ba gaira ba dalili ga kasafin kudi. Wannan ya kawo jinkirin aiwatar da wasu ayyukan raya kasa wadanda ke cikin kudirorin da jam’iyyar APC ta yi wa jama’a alkawarin za ta samar musu idan ta kafa gwamnati, tun can baya da ta na kamfen.
“Ka rika yin amfani da Gidan Saukar Baki na Shugaban Majalisar Dattawa, ka na gudanar da tarukan yi wa jam’iyya zagon-kasa a ciki. A ciki ne ma ka tattara sunayen wadanda suka fice daga jam’iyyar APC.
“Ka karbi wasikar da gungun wadanda suka fice daga APC suka rubuta, kai kuma ka karanta a cikin zauren majalisa a bainar jama’a, cikin har ka ambaci sunan wanda bai kai ga cewa ya fice daga APC ba. Wannan ya tozarta jam’iyya matuka.
“Duk da irin kokarin sasantawar da aka rika yi da masu korafe-korafe, amma sai ka bijire ta rika tara hasalallun cikin jam’iyya, kai ne har da kafa wata kungiyar bijirarrun cikin jam’iyya.”
PREMIUM TIMES ta gano cewa babban na hannun damar Saraki, kuma kakakin yada labaran jam’iyyar, Bolaji Abdullahi bai halarci taron ba.
Discussion about this post