Salisu Nuhu mai shekaru 60 ya kai kukan sa gaban kotun shari’a II dake Kaduna a dalilin danfarar sa na kin aurensa da budurwar sa Janet Baru ta yi.
Nuhu ya bayyana wa kotun cewa ya yi shekara hudu suna tare da Janet da kuma alkawarin auren ta bayan ta musulunta.
” A wannan lokacin duk sanda na ziyarce ta nakan bata kyautan Naira 1000 zuwa 2,000.”
Ya kuma ce ya dunkula Naira 30,000 ya ba Janet domin tabbatar mata da auren ta da yake so ya yi baya wata kawarta mai suna Juliet ta bashi shawarar yin haka.
Nuhu ya kuma ce ya yi wa Janet kyautar Naira 45,000 tare da turmin atamfan Naira 8,000 da kudin dinki Naira 2,000 a lokacin kirisimatin 2017.
” A dalilin haka ina rokon kotu ta tilasta wa Janet ta biya ni kudi na tunda ta fasa auren nawa.”
Janet ta ce Nuhu ya nemeta na tsawon shekara daya ne tak sannan duk kudaden da yake babatun kashe mata duka-duka Naira 75,000 kawai.
Alkalin kotun Musa Sa’ad bayan sauraron su ya daga shari’ar zuwa ranar 17 ga watan Yuli.