Wasu shugabannin yankin Kudanci da Arewa-ta-Tsakiya sun gana tare da tsohon Ministan Tsaro, Theophius Danjuma, dangane da halin da kasar nan ke ciki.
Sun bayyana cewa Najeriya ta shiga cikin wani halin-ha-u-la’i, sai suka roki Danjuma da ya tashi tsaye ya taimaka domin kada kasar ta fada cikin mummunan rikici.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa shugabannin sun kai ziyarar ce a karkashin jagoran dattawan kabilar Ijaw, Edwin Clark, sun nuna fushin su dangane da halin lalacewar matsalar tsaron da kasar nan ke ciki.
Sun ja hankalin cewa Najeriya na kan turbar gangarwa cikin kwazazzabon mummunan rikici idan ba a tashi tsaye aka magance matsalar ba.
Shi ma Shugaban Kungiyar Ohanaeze Ndigbo, John Nwodo, ya shaida wa PREMIUM TIMES ta hanyar wayar tarho cewa, kungiyar ta yanke shawarar tunkarar T.Y Danjuma ne saboda babu ruwan sa da siyasa, kuma ya rike mutuncin sa a bannan dattijon da ke da karfinn fada a ji a kasar nan.
“Mu shugabannin yankin kudu da na Arewa-ta-Tsakiya mu na bi domin ganawa da manyan dattawan kasar nan domin samo sahihiyar hanyar da za a magance kashe-kashen da ake ta yi a kasar nan ba gaira-ba-dalili.”
Ya ce za su ci gaba da yawon neman ganawa da manyan kasar nan daban-daban, da nufin samun masu fada a jin da za su tashi a magance matsalar da ke kawo wa hadin kan kasar nan babbar barazana.
“A kowace rana idan ka shiga soshiyal midiya, banda hotunan gawarwakin da aka kashe a fadan da ba su ji ba, ba su gani ba, babu abin da za ka gani.” Inji shi.
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada shugaban kungiyar, David Umahi, ya ce babu wata jihar da ta yarda ta bayar da filayen ta don a killace makiyaya su rika kiwon shanu.
Akwai Chukwuemeka Ezeife, Ferdinand Agu, Ben Dike, Humphrey Orjiakor, C.R. Eherika, Idongesit Nkanga, Tony Nyiam da Godswill Igali.
Sauran sun hada da: Ayo Adebanjo, Dan Suleman, Olu Falae, Yinka Odumakin, Banjo Akintoye, Broderick Bozimo, Alfred Mulade, Tonye Douglas, Bitrus Dogu, Maryam Yunusa, Tanko Abdullahi, da sauran su da dama.