Hukumar NYSC na shan matsin-lambar bizne harkallar Minista Kemi Adeosun

0

PREMIUM TIMES ta gano wata manakisa da ake kitsawa ta hanyar matsa wa Hukumar NYSC ta bizne harkallar satifiket din Ministar Harkokin Kudi, Kemi Adeosun na bogi.

Tashin farko wannan jarida ta gano cewa wasu manyan jami’an NYSC sun kwarmata wa Minista Adeosun wasikar da jaridar ta aika musu, inda ta nemi sanin ranar da Kemi ta karbi satifiket din na ta.

Dalili na farko shi ne ba da jimawa da aika wasikar a hedikwatar NYSC ba, sai manyan mukarraban Ministar suka fara bin ‘yan rahoto, editoci da shugabannin jaridar sun a yi musu ‘yar-murya.

An shafe kwanaki da dama ma’aikatan wannan jarida na fama da matsin-lambar rokon su da su gina rami, su bizne labarin don kada su yi tonon sililin da zai kwance wa Kemi fatari a tsakiyar kasuwa.

PREMIUM TIMES ta hakkake cewa an kwarmata wa Kemi wasikar da jaridar ta aika hedikwatar NYSC a ranar 1Ga Yuni, 2018.

Daga wannan lokacin ne NYSC ta daina daukar waya ko maida amsar sakonnin tes idan wannan jarida ta huntubi hukumar.

Share.

game da Author