NDLEA ta kama mutane 108, ta hukunta 83 a cikin watannin bakwai

0

Hukumar yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) na jihar Legas ta kama dillalan maiyagun kwayoyi 108 sannan kotu ta hukunta 83 daga cikinsu a tsakanin watannin Janairu zuwa Yuli a jihar Legas.

Shugaban hukumar Sule Aliyu ya sanar da haka wa manema labarai ranar Talata a Legas.

Ya ce muggan kwayoyin da suka kwato hannun wadannan mutane sun hada da ganyen wiwi, hodar ibilis, Exol, Raphynol, tramadol da Diezapam da aka kiyasta ta su kan miliyoyin naira.

” Cikin dillalan muggan kwayoyin 108 da muka kama 106 maza ne sannan biyu mata ne.

A karshe Aliyu ya jinjina wa kokarin da ma’aikatan hukumar ke yi da a dalilin haka suka sami wannan nasarori sannan ya roki mutanen jihar Legas da su taya gwamnati da bayanai kan irin wadannan mutane.

Share.

game da Author