A yau Talata kotun dake Ebute Meta ta gurfanar da wani magidanci mai suna Premie Imafidon mai shekaru 47 kan kashe matarsa Hope mai shekaru 42 da mari.
Lauyar da ta shigar da karar Maria Dauda ta fada a kotun cewa Imafidon ya falla wa matarsa Hope mari ne inda daga nan ko ta yanke jiki ta fadi ta mutu nan take ranar 15 ga watan Yuni da karfe bakwai na yamma a gidan su dake Agege a jihar Legas.
Alkalin kotun A.O. Ajibade ya aika da shari’ar Imafidon fannin gurfanar da masu aikata laifuka irin haka na jihar.
Sannan Imafidon zai yi zaman kurkuku dake Ikoyi har sai kotun ta kammala shawara.
Za a ci gaba da shari’a ranar uku ga watan Satumba.
Discussion about this post