Rundunar ‘Yan sandan Zamfara ta bayyana cewa ta kori wasu mahara kuma barayin shanu yau Talata, a kasuwar Talata-Mafara.
Rundunar ta kara da cewa ta kuma ceto wasu mutane tara da aka yi garkuwa da su.
Kakakin sun a jihar Zamfara, Muhammad Shehu ne ya bayyana haka a cikinnwata sanarwa da ya fitar ga manema labarai, a ranar Talata.
Shehu ya ce maharan sun yi dira cikin kasuwar Talata-Mafara, wadda kasuwar sayar da shanu ce da misalin karfe 4 na yamma da nufin tada hankalin jama’a su kuma su saci shanu.
Maharan inji shi kuma sun yi garkuwa a mutane tara. Sai dai kuma jami’an tsaron da aka girka a gefen kasuwar sun kai musu farmakin hana su kai mummunan harin, kuma suka ceto wadanda suka yi garkuwar da su har mutane tara.
Ya ce an samu makamai a hannun su, kuma su na a hannun ‘yan sanda ana bincike.
Discussion about this post