Kwata-kwata maniyyata 2,800 kacal ne suka samu sukunin iya biyan kudin zuwa Hajjin bana daga kujeru 5,500 din da aka ware wa jihar Kano.
Kakakin Yada Labaran Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Hadiza Abbas ce ta shaida haka ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), yau a Alhamis a Kano.
Ta ce saboda kasa samun sukunin biyan kudin aikin Hajji da Musulmai suka yi a wannan shekarar, hakan ya sa hukumar kara wa’adin biyan kudaden ga wanda zai iya cikawa.
Sai dai kuma ba ta ce ga ranar da za a rufe karbar cikon kudaden ba.
Amma ta shawarci wadanda ke da bukatar cikawa daga cikin maniyyatan da su gaggauta cikawa kafin a fara daukar maniyyatan jihar.
Daga nan ta ce tuni an fara tattara bayanan maniyyatan kuma dukkan wadanda suka biya kudaden su gaba daya za a tantance daukar bayanan kowanen su.
PREMIUM TIMES HAUSA ta gano cewa a shekarar 2016, an samu mahajjata 5, 808 daga jihar Kano.
A shekarar 2017 kuma an samu 6,602.
Da yawa wasu na danganta matsalar tattalin arziki da kuma yadda kudin tafiya aikin Hajji ya nunka a cikin shekara uku.
Gwamnatin Tarayya a shekarar da ta gabata ta bayyana cewa manoma sun samu alheri sun rika tururuwar zuwa aikin Hajji da kara aure saboda alherin ribar noman da suka samu.
Sai dai kuma wani bincike na musamman da PREMIUM TIMES ta gudanar a jihohin Kebbi, da wasu jihohi, ya nuna cewa da dama wadanda ake cewa sun je aikin Hajjin daga cikin wasu manoman, kamfaci kudaden rancen aikin noman da gwamnatin tarayya ta ba su ne suka tafi aikin Hajji, wasu kuma su ka yi ta kara aure.