Zan biya mijina sadakin da ya biya a kaina don mu rabu – Uwargidan Ibrahim

0

Wata matan mai suna Hanifa Adamu ta shigar da kara a kotun dake Magajin Gari a Kaduna tana neman mijin ta mai suna Ibrahim Isyaku ya sauwake mata auren da ke kanta da shi.

Lauyan Hanifa, mai suna Junaidu Aminu ya bayyana cewa Hanifa na neman Isyaku ya sake ta ne domin ta gaji da zaman auren sa saboda ba ta iya ci gaba da yi masa biyayya.

” Sannan Hanifa a shirye take ta mayar wa Isyaku sadakin da ya biya a kanta wato Naira 50,000.”

Shi ko lauyan Isyaku mai suna Badamasi Adamu ya nemi kotu da ta yi watsi da wannan kuka na Hanifa, domin kuwa mijin nata Isyaku baya kasar ya tafi Ummra.

Badamasi ya roki kotu da ta daga zaman shari’ar har sai Isyaku ya dawo daga Ummura.

A karshe alkalin kotun Dahiru Lawal bayan sauraron su ya daga shari’ar sai 15 ga watan Agusta.

Share.

game da Author