Gwamnati Buhari akwai kantara wa ‘yan Najeriya karya – Inji PDP

0

Jam’iyyar PDP ta soki gwamnatin APC da yawan kantara zuki ta malle ga ‘yan Najeriya, wato lafto karya gatse haka kawai.

Kakakin Jam’iyyar PDP Kola Ologbondiyan ya karyata maganganun da mai ba shugaban kasa shawara kan zamantakewa tsakanin ofishin shugaban kasa da majalisar dattawa, Ita Enang cewa da yayi wai duk wadanda suka canja sheka zuwa PDP daga APC zasu yi wa Buhari aiki a zaben 2019.

Ita Enang ya fadi cewa baki-da baki duk wadanda suka canza sheka zuwa PDP sun yi wa Buhari alkawarin cewa duk da sun fice daga jam’iyyar APC zuwa PDP, Buhari za suyi wa aiki a 2019.

Kola ya ce wadannan zantuka da Enang ya furta zuki ta malle ne domin babu irin wannna yarjejeniya da aka yi tsakanin masu canza sheka da shugaba Buhari.

Kola ya kara da cewa idan ba kantara karya ba ta yaya za a ce wai wadannan mutane za su dauki irin wannan alkawari.

” APC kamar kwalakwale ce dake gab da nutse wa a teku, kuma wadanda suka fice daga jam’iyyar sun san da haka, hasali ma shine makasudin ficewar su daga jam’iyyar, sannan kuma wani ya fito ya ce wai sun fito sun ce wai duk da haka za su yi jam’iyyar ne a 2019.

Ya ce hakan ba gaskiya ba ne.

Share.

game da Author