BOKO HARAM: Makon Asarar Sojojin Najeriya

0

Boko Haram sun kai wani farmakin kwanton-bauna kan sojojin Najeriya har sau biyu, inda kwakkwarar majiya ta tabbatar da cewa sun kashe sojoji 17, sannan suka ji wa 18 raunuka.

Rahoton ya kara da cewa cikin wadanda aka kashe din akwai babban jami’in soja daya.

Baya ga wadanda aka ji wa ciwo su 18, Boko Haram sun gudu da manyan makaman yaki da suka hada da manyan bindigogin harbo jiragen sama da motoci kirar Hilux da manyan motocin daukar dakarun yaki.

Ana ganin wannan ne musabbabin yi wa manyan kwamandojin yaki canjin wurin aiki.

Wannan canji da aka yi musu jiya shi ne canji na biyar da aka yi wa kwamandojin yaki tun cikin 2015, bayan hawan Shugaba Muhammadu Buhari mulki cikin 2015.

MAKON ASARAR SOJOJI

za a iya kiran wannan sati makon asarar sojojin Najeriya. Ranar 21 Ga Yuli, an yi asarar sojoji 8 a wani hari da Boko Haram suka kai wa sojojin Bataliya ta 223 a Karamar Hukumar Tarmuwa, jihar Yobe.

Sai kuma wani gumurzu da aka yi a ranar 24 Ga Yuli, a Damboa, inda aka rasa sojoji shida, aka jikkata 14.

Sai kuma wani harin da Boko Haram suka kai a garin Jagana, kilomita 50 daga Maiduguri kan titin zuwa Kano.
A wannan hari ma an yi asara kuma rahotanni sun ce an gudu da kayan fama.

Ko fadan Jagana dai hukumar tsaro ta sojoji ba ta bayar da labarin faruwar sa ba, har sai da PREMIUM TIMES ta buga tukunna.

Share.

game da Author