Shugaban Kasar Faransa, Emmanuel Macron, ya bayyana cewa Faransa ba ta iya magance wa Najeriya ko Afrika dungurugum matsalar tsaron da suka addabe su.
Ya ce mafita ita ce kawai Gwamnatocin Afrika su tashi tsaye su fatattaki ‘yan ta’adda kawai.
Shugaban na Faransa ya yi jawabin ne a lokacin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai tare da Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, a ranar Talata, fadar Shugaba Muhammadu Buhari.
Da ya ke amsa tambaya kan ko me Faransa za ta iya yi wajen taimaka wa Najeriya magance matsalar tsaro?
Sai Macron, ya kada baki ya ce, “Da farko dai, ni ina tunanin cewa wannan gagarimin shiri ne, na shugabannin Afrika, ba Faransa ce za ta magance matsalolin tsaron Afrika ba.”