BASHI: Kamfanin bada wutar lantarki ya yanke wutar Gidan Gwamnatin Jihar Imo

0

Kamfanin bada wutar lantarki ya datse wutar Gidan Gwamnatin Jihar Imo, saboda kasa biyan bashin wutar naira miliyan 200 da ta sha.

Haka kuma kamfanin ya yanke wutar Sakateriyar Gwamnatin Jihar Imo duk saboda taurin bashi.

Haushin wannan ne ya sa ofishinn kula da tsarin gine-gine na jihar Imo ya yi wa ofishin bayar da wutar jan fentin da ke nuna za a ruguje shi gaba daya.

Yayin da wakilin PREMIUM TIMES ya isa hedikwatar kamfanin lantarkin, EEDC da ke kan titin Royce a Owerri, ya samu an rigaya an masa rubutu da jan biro mai nuna umarnin a rushe ginin gaba dayan sa a cikin kwanaki bakwai kacal.

Kakakin Hukumar, Emeka Ezeh ya tabbatar da faruwar datse wuta da suka yi wa gidan gwamnatin, amma dai gwamnatin na ta kai gwauro ta kai mari wajen kokarin ganin an biya bashin wutar.

Ya kuma ce su na sane da cewa an zana wa ofishin su jan fenti an kuma rubuta umarnin za a ruguje shi cikin kwanaki bakwai. Sannan ya kara tabbatar da milyoyin kudaden da suke bin Sakateriyar Gwamnatin Jiha da kuma ofishin gwamna.

Share.

game da Author