Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa(INEC), ya fito karara ya ce babu wani ma’aikacin hukumar sa da zai iya yin magudi ko murde zaben gwamnan jihar Ekiti, kamar yadda wasu ke zargi.
Mahmood Yakubu ya bayyana haka a yau Laraba, yayin da ya ke ganawa da jam’iyyun siyasa a Cibiyar Zabe ta INEC, a Abuja.
“Ina tabbatar muku da cewa tsarin zaben da muka shigo da shi ya wuce tunanin wani ko ma wane ne ya yi magudi ko ya murde sakamakon.”
Yakubu ya ce an dauki tsauraren matakan da zai iya cewa idan dai wani zai iya murde zaben to rakumi zai iya shiga ta kofar allura ya fita.
“Zargin da wasu ke yi wai an kwafi katin rajista da kuma na’urar karanta katin kada kuri’a, wannan duk shaci-fadi ne kawai.”
Tun da farko a jawabin nasa, Yakubu ya fara ne da shaida wa shugabannin jam’iyyun da ya gana da su irin shirin da INEC ta yi na gudanar da zabukan cike gurbi a jihohin Bauchi, Katsina, Taraba da wasu wurare.
Daga nan sai ya gangara kan zaben gwamnan jihar Ekiti, da ya ce za a gudanar a rumfunan zabe 2,195 da ke cikin mazabu 177 a fadin jihar.
Ya ce dukkan fadin kananan hukumomin jihar 17 za a gudanar da zaben, wanda ya ce jam’iyyun siyasa 35 suka za su shiga zaben.
Discussion about this post