Tursasa yaro ya ci abinci dole na hana shi girma yadda ya kamata – Bincike

0

Wasu likitocin yara a jami’ar Michigan dake kasar Amurika sun yi kira ga iyaye da su daina tursasa wa ‘ya’yan su dole sai sun cin abinci.

Likitocin sun bayyana cewa yin hakan na lalata dangantakar dake tsakanin iyaye da ‘ya’ya sannan hakan na sa su ki cin abinci ko kuma suce sai sun zabi abincin da za su ci.

Likitocin sun gano haka ne a binciken da suka gudanar domin gano ko tursasa wa yaro ya ci abinci na da amfani ko a’a.

” Sakamakon da muka samu ya muna cewa mafi yawan yaran da ake tursasa musu basa zama acici sai dai tsagina ginin abincin suke yi.

” Hakan na da nasaba ne sanadiyyar tursasa musu da iyayen su ke yi a duk lokacin da za su ci abinci wanda hakan ke hana su yin girma yadda ya kamata.

A karshe Likiocin sun ce idan har ya zama sdole sai an tilasta wa yaro ya abinci cin abinci a yi haka da dabara amma ba a bashi tsoro ba.

Share.

game da Author