‘Yan Majalisar Wakilai 36 a yau suka fice daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP da ADC.
Da ya ke sanar da ficewar ta su, Kakakin Majalisa Yakubu Dogara, ya bada misalan da suka bayar da cewa matsaloli sun ki ci sun ki cinyewa a cikin APC.
34 daga cikin su a PDP suka koma, yayin da ADC kuma ta karbi hudu.
Wasu daga cikin wadanda suka fice daga APC zuwa PDP, sun hada da: Hon. Ali Madaki, Sani Rano, Dickson Tackghir, Hassan Saleh, Mark Gbilah, Damburam Nuhu da Rasak Atunwa.
Akwai kuma irin sure Abdulsamad Dasuki, Zakari Mohammed.
Yakubu Dogara da Yusuf Lasun mataimakin sa ba su furta komawar sure kowace jam’iyya ba.
Sannan a daidai za a watse daga majalisa sai Honarabul Orker Jev ya bayyana cewa shima ya hakura da APC din haka nan. Ya bi ‘yan uwan sa macu canza sheka.
Idan ba a manta ba sanatoci 15 ne suka koma jam’iyyar PDP a majalisar dattawa duk a yau Talata.