Uwargidan gwamnan jihar Kebbi Zainab Babudu ta bayyana cewa gwamnati ta ware Naira miliyan 105 domin tallafawa kungiyoyin mata 200 da jari dake kananan hukumomi 21 dake jihar.
Zainab ta fadi haka ne ranar Litini a taron kadamar da wani shiri na tallafa wa kungiyoyin mata da aka fara a Birnin Kebbi.
Ta ce shirin zai tallafa wa kungiyoyin matan da kudade na jari.
” Kananan hukumomin da za a fara da su sun hada da Augie, Arewa, Bagudo, Birnin Kebbi, Bunza, Sakaba, Danko/ Wasagu da Ngaski.
” Su wadannan kudade za a bayar da su ne mata su sami jari, sannan idan sun tashi dawowa dashi uwar kudin kawai zasu dawo da.
Zainab ta ce gwamnati ta yi haka ne domin kawar da talauci a tsakanin mata da sauran mutanen jihar.
Daga karshe gwamnan jihar Atiku Bagudu ya jinjina wa wannan kokarin na uwargidan sa.
A wannan jari dai ko wacce mace za ata sami Naira 15,000 da ‘yan kayan sana’a.