Kwankwaso, Hunkuyi, Nazifi da wasu santoci 13 sun koma PDP

0

A yau Talata ne wasu sanatoci wanda ‘yan asalin jam’iyyar APC ne suka canza sheka daga jam’iyyar su ta asali zuwa jam’iyyar PDP.

Kwankwaso da ‘yan uwan sa sanatoci 14 sun bayyana haka ne yau a zauren majalisar a wasika ta bai daya da suka saka wa hannu.

Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ne ya karanta wasikar a zauren majalisar.

Bayan haka majalisar ta tafi hutu sai 25 ga watan Satumba.

Ga sunayen wadanda suka canza shekar

Sen. Tejouso
Sen. Shaaba
Sen. Gemade
Sen. Melaye.
Sen. Shittu
Sen. Rafiu
Sen. Shitu Ubali
Sen. Isa Misau
Sen. Hunkuyi
Sen. Monsurat
Sen. Danbaba
Sen. Nafada
Sen. Nazif
Sen. Kwankwaso
Sen. AbdulAziz Nyako

Share.

game da Author