Na shiga siyasa don kawo karshen almajiranci – Ndi Kato

0

Wata matashiyar ‘yar siyasa mai suna Ndi Kato daga jihar Kaduna, ta ce da zarar burin ta ya cika aka zabe ta matakin majalisar dokokin jihar Kaduna, to farkon abin da za ta yi shi ne kawo kudirin a kafa dokar hana barace-baracen da kananan yara ke yi da sunan almajiranci.

Kato ta fadi haka ne a wata tattauanawa da ta yi da PREMIUM TIMES.

Ta ce da yawa da kyakkyawar manufa suke tura ‘ya’yan su almajirci. “To amma a yanzu abin ya sauya, an maida kananan yara su na rayuwa cikin kangin bauta ne kawai.

Ta kara da cewa sannan kuma za ta kira wani kudiri da zai sa a kafa dokar cewa ilmin yaro daga ajin raino har zuwa firamare ya zama tilas ga iyaye su bar ‘ya’yan su a koyar da su ilmi.

Daga nan ta ci gaba da cewa ta na da muradin rage radadin talauci da kuma samar da tsare-tsaren zaman lafiya a tsakanin juna.

Kato ta nuna takaicin yadda yara a Arewa ke wata irin ratuwa tamkar lokacin kangin bauta wai da sunan almajirci.

Ta ce lokaci ya yi da almajirai za su zauna wuri daya su nemi ilmi domin akasari ya na na fadawa mawuyacin.

Ta koka da rashin mace ‘yar majalisar dokoki a fadin jihohin Arewa ta Yamma.

Share.

game da Author