Mafi alheri ga ‘yan Najeriya shi ne kada jirgin Nigeria Air ya iya tashi sama – Oby Ezekwesili

0

Tsohuwar Ministar Ilmi, Oby Ezekwesili, ta yi kirdadon cewa jirgin Najeriya ba zai taba samun fukafikin da zai iya tashi sama ba. Kuma ta yi fatan kada ya iya tashi sama.

“Ai shirin ba zai yi nasara ba”, inji Ezekwesili a shafin ta na Twitter, a ranar 28 Ga Maris, watanni hudu kafin kaddamar da hoto da fentin jirgin a Farnborough da ke Ingila.

“Ko don kasar mu wannan jirgi ba zai yi nasara ba, domin rashin nasarar ta sa, alheri ne ga kasar mu.” Haka ta rubuta a shafin ta na twitter.

Ta ci gaba da cewa kafa wani sabon kamfanin zirga-zirgar sufurin jiragen sama asara ce, wofintar da dukiya ne, kuma ba shi ne jama’a suka fi so ba.

Wannan furuci na ta ya haifar da ka-ce-na-ce, a Najeriya inda jama’a da dama suka rika nuna cewa ba ta fatan ci gaban kasar nan.

Wata mata mai suna Hafsat Hadi, ta maida mata raddin cewa, “Mama, idan ki ka ce kafa kamfanin jirgin asarar kudi ne, zan iya yarda da ke. Amma kuskure ne ki hakikice cewa wai tilas ne ma ya ruguje ko ya shiririce, wannan wauta ce, cin fuska ne a gare mu, gara ma ki tuba, ki ba mu hakuri kawai. Ya kamata ki sauke girman kai, ki nemi afuwar mu.”

Sai dai kuma wannan duk bai sa Ezekwesili ta saduda ba, sai ma ta kara bude wuta.

“Kafin a kai ga sake kamfatar kudi a zuba cikin ramin da ba za a iya kwaso ba ko ba za a iya dawo da su ba, da sunan wai kamfanin zirga-zirgar jirage, to ko ni kadai za a bari dai ban goyi bayan haka ba.”

A cikin wani sakon twitter da ta kara turawa, ta ce Najeriya ba ta da nasibi ko tasirin albarkar kasuwancin harkokin sufurin jiragen sama.

Sai dai kuma Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, ya bayyana cewa ba da kudin Najeriya za a sayo jiragen.

Najeriya za ta karbo jirage biyar na farko da za a fara jigila da su a ranar 19 Ga Disamba, sauran 25 kuma za su shigo cikin shekaru biyar.

Share.

game da Author