Wata kauye mai suna Damaru dake karamar hukumar Soba a jihar Kaduna ta dauki matakin inganta kiwon lafiyar mutane kauyen ta hanyar hukunta masu bata gari da gurbata muhalli.
Dakacen Damaru Adda’u Ibrahim ya bayyana haka wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Alhamis a kauyen Damaru.
Bisa ga bayyanan da ya yi Ibrahim yace matakan da suka dauka sun hada da cin duk wanda aka kama yana bahaya a fili tarar Naira 200 ko kuma bulala bakwai tare da kwashe kashin da aka kama shi yana yi.
Ibrahim ya ce daukar wannan mataki ya zama dole ganin cewa mutanen garin musamman yara kanana na kamuwa da cututtuka dabam-dabam saboda rashin tsaftace muhallin mu.
Ya ce yanzu komai ya yi sauki a dalilin wayar mana da kai da shirin SHAWN yayi wa mutanen garin mu.
‘Yanzu za adinga yin aikin gayya don tsaftace muhalli a wannan gari duk karshen mako. sannan za a ci gaba da wayar wa mutane da kai game da muhimmanci tsaftace muhalli.
A karshe wasu mazaunan kauyen kamar su Zaitu Mai-Unguwa, Maliya Abubakar, Gambo Yusuf sun jinjinawa gwamnatin jihar Kaduna saboda kawo musu wannan shiri da suka amfana da shi matuka.
Shirin SHAWN shiri ne da hukumar DFID, UNICEF da gwamnatocin jihohin Kaduna, Katsina, Zamfara, Benue, Bauchi da Jigawa suka tsara domin wayar da kan mazauna yankunan karkara kan mahimmancin tsaftace muhalli.
Discussion about this post