Sabuwar jam’iyyar APC ta Hakika wato R-APC da wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyyun PDP,SDP da wasu sun amince suyi aiki tare wajen kayar da APC a zaben 2019.
Shugaban jam’iyyar Buba Galadima ne ya jagoranci wasu daga cikin ‘ya’yan kungiyar zuwa wannan zama don amince wa da yarjejeniyar.
Cikin wadanda suka halarci taron a bangaren jam’iyyar PDP akwai mataimakin shugaban majalisar dattawa Ike Ekweremadu, akwai gwamnan jihar AkwaIbom Urtom Udom, sannan akwai tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar sannan kuma sanata Dino Melaye ma ya na cikin tawagar da suka halarci taron.
Ben Obi da shine sakataren wannan zama ya bayyana cewa dole ne ayi wa zaben 2019 shiri na musamman domin gumurzu ne za ayi tsakanin duhu da haske a 2019.