Gwamnonin Kudu-maso-gabas sun ki amincewa da killace makiyaya a jihohinsu

0

Gwamnonin Jihohin Kudu-maso-gabas sun bayyana cewa ba za su amince da tsarin bayar da kasar su a killace makiyaya wuri daya ba, watau ‘ranching’ a fadin jihohin su.

Gwamnonin sun fadi haka ne a Enugu bayan tashi daga wani taron gwamnonin shiyya da suka gudanar, a Enugu a ranar Lahadi da dare.

Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da na Enugu Ifaeanyi Ugwuanyi, na Ebonyi, David Umahi, sai gwamnonin Abia da Anambra suka turo mataimakan su a matsayin wakilan su.

Sai dai kuma gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha bai halarci taron ba. Shi ma mataimakin sa, Ezeakonobi Madume, wanda suke faman sa-toka-sa-katsi a tsakanin su, bai samu halarta ba.

Okorocha ne kadai gwamnan da ba PDP ba yankin, da ke karkashin jam’iyyar mai mulki, APC.

Da ya ke wa manema labarai jawabi bayan kammala taron, Shugaban Kungiyar Gawamnonin Shiyyar, David Umahi, ya ce gwamnonin sun amince da babbar murya daya cewa ba su yarda a yi tsarin kiwon shanun da gwamnati ke son fito wa makiyaya Fulani da shi ba a yankin su.

Umahi ya ce ba gaskiya ba ne da gwamnatin tarayya ta ce jihar sa ta amince da tsarin.

Ya kara da cewa jihohin yankin su na kashe makudan kudade wajen biyan diyyar barnar da makiyaya ke yi sanadiyyar karakainar da makiyaya ke yi da dabbobi idan suka tashi daga nan zuwa can.

Don haka ya ce zasu kira taron neman mafita inda za su zauna da jami’an tsaro a samu hanyar shawo kan wannan matsala.

Share.

game da Author