Yadda Ministoci da manyan jami’an gwamnatin Buhari suka handame tallafin karatu da Kamfanin CCECC ya ware wa matasa

0

Rincimi, hargowa, fushi da tofin Allah-tsine sun barke a Harabar Ma’aikatar Sufuri ta Kasa jiya Laraba a Abuja.

Rudanin ya faru ne bayan da dafifin matasan da suka yi tafiyayya daga garuruwa daban-daban suka mamaye ma’aikatar da nufin zuwa mika fam din da kowanen su ya cika, domin neman tallafin gurbin karatun da shahararren kamfanin gine-ginen titina na China ya ware wa matasan kasar nan.

Kamfanin mai suna China Civil Engineering and Construction Corporation, da aka fi sani da CCECC, a yanzu ya na a sahun gaba na kamfanonin kasashen waje da ke gudanar da manyan ayyukan kwangiloli a fadin kasar nan, baya ga kamfanin Julus Berger.

Amma maimakon a yi wa matasan shimfidar fuska, sai jami’an gwamnati a Ma’aikatar Harkokin Sufuri ta bayyana wa dafifin matasan nan cewa ai sam babu wata maganar bayar da tallafi, ba su san ta ba.

Wannan ya harzuka matasan, har ta kai su ga yin shinge, suka tare motoci, suka hana su wucewa.

Domin a kauce wa barkewar rikici ganin yadda matasan suka harzuka sosai, sai Babban Sakatare na Ma’aikatar Sufuri, Sabiu Zakari ya fitar da takarda ga manema labarai, ya bayyana cewa duk wanda ya ce kamfanin aikin titin jiragen kasa na CCECC na raba tallafin gurbin karatu ga matasa, to karya ne, kuma zamba ce kawai ake neman a yi musu.

Sai dai kuma wasu da suka san gaskiyar lamarin, sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa bayanan da Babban Sakataren ya yi, ba gaskiya ba ne, akwai maganar a kasa, sai dai idan ba za su ba matasan tallafin ba ne kawai.

“Tabbas ina sane da cewa kamfanin CCECC, wanda ke aikin gina tagwayen titinan jirgin kasa daga Lagos zuwa Kano, ya tuntubi Ma’aikatar Sufuri , ya sanar da ita anyar sa ta daukar nauyin wasu matasa a Najeriya domin su fita su yi karatun digiri a kan fasahar aikin jirgin kasa a Chana.”

Haka wani babban jami’i ya shaida wa PREMIUM TIMES, amma ya ce kada a bayyana sunan sa, gudun kada a yi masa bi-ta-kulli.

Maimakon Ma’aikatar Sufuri ta yi sanarwa ta hanyar buga tallace-tallacen kiran matasa su fito su cika fam, sai ma’aikatar ta rika tuntubar kusoshin gwamnatin Buhari, ta na cewa kowa ya kawo wanda ya ke so a dauka domin cin gajiyar guraben karo ilimin.

Hakan ne ya sa duk wani mai neman wannan tallafi, idan dai ba shi da wata alaka da ministoci da wasu manyan masu kumbar susa a cikin gwamnati, duk aka hana su samun wannan damar.

Wani da ya san duk irin tsiyar da ake kullawa a cikin ma’aikatar, ya shaida wa Premium Times cewa, daga cikin wadanda aka ce su kawo sunayen matasa akwai ministoci, manyan sakatarorin gwamnati, jami’an da ke aiki ofishin Shugaban Kasa da kuma wasu zababbun ‘yan majalisar tarayya.

Daga wanda ya bada sunan dan sa, sai wanda ya bada sunan kanen sa, sai sunayen ‘ya’yan dangi da kuma sunayen ‘yan uwan matan su.

PREMIUM TIMES HAUSA ta samu kwafen takardar da a can baya Zakari ya rubuta wa Ministan Kasuwanci da Masana’antu, Okechukwu Enelamah, inda ya ce ya kawo sunayen wadanda ya ke so su ci gajiyar guraben karo ilmin.

Ya rubuta wasikar ne a ranar 7 Ga Yuni, 2018.

Bayan kwana uku kuma, wato a ranar 11 Ga Yuni, Zakari ya sake tunatar da ministoci da sauran wadanda ya aika wa wasika cewa, ga irin abubuwan da matasa dangin su da dangin matan su da suka zaba za su tura domin a dauke su aiki.

Daga cikin abin da wasikar ta nema, akwai bayanan makarantun da yaro ya yi, da kuma gari da jihar da aka haife shi. An kuma nemi su kai hotuna a ofishin sa, kafin ko kuma a ranar 20 Ga Yuni, 2018.

Zakarin da ya rubuta takardar sanarwar watandar guraben karo ilmi ga ministoci da manyan jami’an gwamnatin Buhari, shi ne dai Zakarin da a jiya Laraba da dare ya rubuta wa ‘yan jarida takardar bayanin cewa ba su ma san da batun bayar da guraben karo ilmin ba.

PREMIUM TIMES ta yi kokarin jin ta bakin Minista Enemalah, amma wayoyin sa a kulle. An tura wa kakakin yada labaran sa tes, amma har yanzu Constance Ikoku bai amda kira ba, bai kuma maido amsar tes din da aka yi masa ba.Wani abin mamaki shi ne, duk da yadda aka rika daukar ‘ya’yan na jikin gwamnati a asirce, maganar tallafin ta fito fili, har ‘ya’yan talakawa suka rika tururuwar neman cika fam.

An dai tsara cewa za a yi intabiyu domin tantance wadanda za a dauka yau 21 zuwa 22 Ga Yuni, a hedikwatar kamfanin CCECC da ke Abuja.

Premium Times ta tattauna da matasan da suka yi dafifi jiya a Ma’aikatar Sufuri, inda da yawa daga cikin su suka nuna takaicin rashin adalcin da suka ce an nuna musu.

Daruruwan matasa dai ne suka yi wa ma’aikatar dafifi.

Share.

game da Author