Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), ta musanta zargin da wasu ke yadawa cewa ta nuna goyon bayan ta a kan tazarcen Shugaba Mhammadu Buhari.
Har ila yau, ta kuma karyata zargin cewa ta na goyon bayan Adams Oshimhole a matsayin shugaban jam’iyyar APC.
Shugaban CAN ta Najeriya, Samson Ayokunle ne ya yi wannan martanin, ganin yadda wasu kafafen yada labarai suka yada cewa CAN ta nuna goyon baya ga Buhari da kuma Oshiomhole.
A cikin wata takarda da kakakin yada labaran sa Adebayo Oladeji ya sa wa hannu a ranar Laraba, ya ce wadannan surutan duk ba gaskiya ba ne.
Sai dai kuma ya ce wata kungiya ce mai suna wanda ya yi kama da “CAN” ta fitar da sanarwar goyon bayan.
Sunan kungiyar dai “Chabge Advocates of Nigeria”, wato CAN a takaice, wadda kuwa ba ita ce kungiyar kiristocin Najeriya ba.
Saboda haka ya ce jama’a su yi watsi da wancan tunanin da suke yi cewa kungiyar kiristoci ta CAN ce ta fitar da sanarwar goyon bayan.
Discussion about this post