SHARI’AR EL-ZAKZAKY: ’Yan sanda sun hana motoci bin manyan titinan garin Kaduna

0

An rufe ilahirin manyan titinan garin Kaduna, musamman da ke kan babban titin Indepence Way a yau Alhamis, saboda gabatar da Sheikh El-Zakzaky kotu a ci gaba da shari’ar sa a karo na biyu a yau.

A yau ma kamar a karon farko, an hana ‘yan jarida shiga kotun domin daukar rahoton yadda shari’ar ta kaya.

Kamfanin Dillancin Labarai ya ruwaito cewa an datse titi, an hana motoci wucewa daga kan titin Independence daga Kabala West har zuwa mahadar titi na Waff Road.

Haka dukkan motocin da ke nufin hawa kan titin Independence da suka fito da Kaduna Polytechnic, duk an hana su hawa Independence Way.

Su ma wadanda suka fito daga Yakubu Gowon Way, an hana su danganawa zuwa titin da hedikwatar ‘yan sandan jihar ta ke. An kuma hana masu mota karasawa bankunan First Bank, Wema Bank da kuma Access Bank.

NAN ta ruwaito cewa an yi taho-mu-gamu tsakanin mabiya El-Zakzaky da ‘yan sanda jiya a Kaduna, yayin da suka yi zanga-zangar nuna a saki jagoran na su.

Ana tsare da malamin tun cikin watan Disamba na 2015, bayan da kotu ta bada umarnin a sake shi, ba sau da yaba tun a cikin 2016.

Share.

game da Author