Babbar Kotun Jihar Jigawa mai zama a Dutse, ta sallami tare da korar shari’ar da ake yi tsakanin tsohon gwamnan jihar, Sule Lamido da Gwamnatin Jihar Jigawa.
Gwamnatin jihar cwe ta maka Sule Lamido kotu, inda aka zarge shi da tunzura jama’a su tayar da fitina, bata suna da kuma laifin kawo barazana ga zaman lafiyar jihar, cikin sherakar da ta gabata.
Lauyan Sule Lamido, Yakubu Ruba ne ya kalubalanci wannan tuhuma da ake yi wa tsohon gwamnan.
Lamido dai a yanzu shi ne a sahun gaba na msu neman kujerar shugabancin kasar nan a zaben 2019, karkashin tutar PDP.
Tun da farko dai a Kotun Majistare ta Dutse ce, aka fara shari’ar, inda bayan lauya Ruba ya kalubalanci kotun, a kan rashin sahihin dalilin tuhumar wanda ya ke karewa, inda bayan an dauki lokaci ana shari’a, Ruba ya daukaka kara zuwa Babbar Kotun Dutse.
A hukuncin da alkalan kotun uku suka zartas jiya Lahadi, Mai Shari’a Ahmed Gumel, Umar Sadiq da Abdulmumin Suleiman, duk sun yi watsi da caje-caje da gwamnatin jihar Jigawa ke wa Sule Lamido.
Kakakin gwamnatin jihar Jigawa, Bello Zaki, ya ce ba za a daukaka kara ba.