AIKIN MALUNTA A KADUNA: Hukumar SUBEB ta saki sakamakon jarabawa

0

Hukumar Kula da makarantun Firamare na jihar Kaduna SUBEB ta sanar cewa ta saki sakamakon jarabawar da masu neman aikin malunta suka yi a jihar.

Idan ba a manta ba masu neman aikin malunta a jihar Kaduna sun rubuta jarabawar neman aikin a karo na biyu bayan wadanda suka nema a farko sun fara aiki.

A shelar da gwamnati ta yi, tayi kira ga wadanda suka nemi aikin da su je kananan hukumomin su domin duba sunayen su.

Bayan haka hukumar ta umarce su da su halarci jarabawar gwaji na baki da tantance takardun su da za ayi daga ranar 2 zuwa 7 ga watan Yuli a kananan hukumomin da aka nemi aikin.

“ Duk wanda zai zo gwajin ya tabbata ya taho da takardun shaidan kammala karatun sa da hoto wato fasfot guda biyu.” Inji hukumar.

Share.

game da Author