RASHA 2018: Senegal ta ga samu ta ga rashi

0

An fitar da kasar Senegal daga gasar cin Kofin Duniya da ake fafatawa a kasar Rasha, bayan Columbia ta ci ta kwallo daya mai ban-haushi.

Babban abin ban-haushin shi ne makin su daya da Japan, sai dai kuma FIFA ta yi amfani da baubawan-burmin hukunci, aka fitar da Senegal.

An yi amfani da kungiyar da ta fi aikata yawan laifuka a yawan wasanni da suka yi. An gano cewa an bai wa Japan katin gargadi har guda hudu, yayin da ita kuma Senegal an ba ta har guda shida.

Ganin cewa Senegal ce aka fi bai wa yawan katin gargadi, sai aka ce Japan ta tsallake zuwa rukuni nag aba, yayin da Senegal kuma aka maida ta gida.

Columbia Vs Senegal

Columbia Vs Senegal

Sai dai kuma tun a hutun rabin lokaci Senegal ta samu bugun daga kai sai mai tsaron gida, amma alkalin wasa ya yi musu irin abin da aka yi wa Najeriya.

Bayan da alkalin wasa ya sheka da gudu ya tuntubi bokan da ke wa FIFA duba, ta hanyar talbijin mai gani-har-hanji, sai aka ce Columbia ba ta yi laifi ba don haka ba bugun daga kai sai mai tsaron gida ba ne.

A yanzu dai duk an dawo da kasashen Afrika biyar zuwa gida, babu wadda ta haye zuwa rukuni na biyu.

Share.

game da Author