Masu rajin kare dimokradiyya sun yi raddi kan bai wa Kingibe lambar GCON

0

Masu rajin kare dimokradiyya a fadin kasar nan, sun maida martani dangane yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya hada da sunan Babagana Kingibe a cikin wadanda aka karrama da lambobin girmamawa tare da Abiola da Gani Fawehimi.

Kingibe shi ne mataimakin shugaban kasa na marigayi MKO Abiola, a zaben 12 Ga Yuni, 1993, wanda ba a bayyana wanda ya yi nasara ba.

Yayin da wasu ke ganin cewa Kingibe bai cancanci a ba shi lambar ba, domin bayan an tsare Abiola a kurkuku, Kingibe ya butulce masa, ya shiga gwamnati, har Abacha ya ba shi mukamin Ministan Harkokin Kasashen Waje.

Wasu kuma sun hakkake cewa ai tunda shi ne ya tsaya masa dan takarar mataimakin shugaban kasa, to abin da y ace garin Doma ai ba zai bar garin Awai ba. Don haka shi ma Kingibe ya cancanci karbar lambar girmamawar.

Ya rike wannan mukami tsakanin 1993 har zuwa 1996.

A ranar Laraba ce aka bai wa Abiola lambar GCFR, shi kuma Kingibe da Gani Fawehinmi aka ba kowanen su GCON.

Wannan lambobi da aka ba su dai ba a bai wa kowa sai wanda ya yi shugabancin kasa ko mataimakin sa kawai.

A yau Talata ne aka yi bikin bada lambobin a Fadar Shugaban Kasa Muhammdu Buhari.

Igini, Kwamishinan Zabe na Kasa ne, ya ce ‘’duk wadanda suka ci amanar Najeriya da wadanda suka saida kasar an san su, kuma za su gamu da sakayyar da ta dace da su.”

Ya ce sun gamsu da lambar girmamawa da aka bai wa Abiola da Gani matuka. Ya kuma ce ba za su manta ba a lokacin rugumutsin hayaniyar bayan zaben 12 Ga Yuni, 1993, an yi asarar rayukan ‘yan jarida, har sai da ta kai an koma ana buga jaridu a wajen kasar nan.

Shi kuwa Liborous Oshoma, wani lauya kuma dan rajin kare dimokradiyya, cewa ya yi bai wa Kingibe lambar girmamawa sam bai dace da akidar da ta kafa fafutikar 12 Ga Yuni ba.

“Ya ce baya ga zaben na 12 Ga Yuni, akwai kuma akidanci da ya jinu a cikin zuciya, jini, bargo da kashin ‘yan Najieriya. Amma Kingibe ba shi da wannan akida ko kadan a jini da jijiyar sa. Sai dai kuma tabbas duk ma ta inda za a fassara tarihin 12 Ga Yuni, to ba za a raba Kingibe da tarihin 12 Ga Yuni ba.

Nelson Ekujumi kuwa cewa ya yi, idan dai ana batun karbar ladar sakamakon 12 Ga Yuni ne, to duk abin da ya kamata a ba Abiola, shi ma Kingibe ya cancanci a ba shi.

Nelson ya ce sai fa idan Kingibe din ne da kan sa ya ce ba ya so a kai kasuwa, to shi ne kuma wata magana daban.

“Kai ko da mutuwa Kingibe yay i shi ma, to ya cancanci a ba shi kamar yaddda aka bai wa Abiola.

Daga nan sai ya ce ya kamata mutane su daina alakanta batun 12 Ga Yuni da Abiola shi kadai.

Share.

game da Author