Buhari ya nemi gafarar iyalan MKO Abiola

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bada hakuri ga iyalin Mashood Kashimawo Olawole Abiola dangane da soke zaben 12 Ga Yuni, 1993 da aka yi, wanda aka yi ittifaki cewa Abiola ne ya lashe zaben.

Buhari ya nemi wannan gafara ce a ranar Talata yayin da yake bada lambar girmamawa ta kasa ga Abiola, Babagana Kingibe da Gani Fawehinmi a Fadar Shugaban Kasa, a Abuja.

Tsohon Shugaban Kasa na Mulkin Soja, Ibrahim Babangida ne ya soke zaben, wanda har aka hambare shi ba a bayyana hakikanin wanda ya yi nasara ba.

Buhari ya kara cewa wannan batu ko bikin bayar da lambar girmamawa ba a kirkiro ta don a fama tsohon mikin da aka yi wa wasu a baya ba, amma an yi ne domin a gina kabari a binne duk wata kiyayya, damuwa da kunci ko bacin ran da ke tattare da zaben 12 Ga Yuni.

Daga nan sai ya yi kira ga dukkan ‘yan Najeriya a fadin kasar nan su karbi soke zaben 12 Ga Yuni da aka yi a matsayin kaddara, su karbe shi da zuciya daya.

BUHARI YA WARKE MANA MIKIN ZUCI – Hafsat Abiola

Daya daga cikin ‘ya’yan marigayi MKO Abiola, Hafsat Abiola, ta bayyana cewa abin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa iyalin Abiola za su iya cewa ya warke musu da duk wani mikin da aka yi wa mahaifin su wajen soke zaben 12 Ga Yuni, 1993 da aka yi.

Hafsat ta ci gaba da cewa, ba a kan iyalan Abiola kadai, duk wani dan Najeriya mai fama da mikin zaben 12 Ga Yuni tsawon shekaru da dama, to a yau Buhari ya warkar masa da wannan mikin.

Buhari ya bai wa Abiola lambar girmamawa mafi daraja ta kasa, wadda sai shugaban kasa kadai ke da ita, wato GCFR.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN ya ruwaito cewa yayan Hafsat, Kola ne ya gayyace ta da ta yi jawabi a madadin iyalan Abiola a wurin bikin bada lambar girmamawar, cikin Fadar Shugaban Kasa, a Abuja.

YADDA ABIOLA YA KASA TILAWAR JAWABIN DA YA YI NIYYAR YI WA ‘YAN NIJERIYA –Hafsat Abiola

“Mahaifiya ta ta shaida min cewa Abiola ya sha tsayawa a gaban madubi, ya na tilawar karanta jawabin da zai yi wa ‘yan Najeriya, saboda tun a lokacin da ake ta samun sakamakon zabe, ya hakkake cewa shi ke da nasara, kuma sai ya yi jawabi.

“Kun san Abiola ya na da in’ina. To da ya fara cewa, “Ya ku ‘Yan Najeriya….” Sai ya kakare, bai taba wuce wadannan kalmomi ba.

“Ko ya so kara wasu kalmomi a gaba, ba ya iya cewa komai, sai ya kakare, ko ya fada din ma sai ya sake daga farkon ‘Ya ku ‘Yan Najeriya’.

Hafsat ta ci gaba da cewa mahaifin su ya na shaukin kaunar Najeriya sosai fiye da tunanin mai tunani.

Ta ce Abiola ya fara tsayawa a gaban madubin domin yin tilawar karanta jawabin da zai yi wa ‘yan Najeriya tun lokacin da aka fara fito da sakamakon zabe daga yankunan kasar nan daban-daban, kuma tabbatattun kididdiga na nuna cewa nasara a kan sa ta ke.

Share.

game da Author