Dalilin mu na kin kafa sabbin ‘yan Kwamitin Amintattu – PDP

0

Jam’iyyar PDP ta bayyana dalilan ta na kin kafa sabbin ‘yan Kwanitin Amintattun jam’iyyar, ta na mai cewa ba za ta taba yin abin da ya kaucec wa dokar kasa da dokar jam’iyyar PDP ba.

Shugaban Kwamitin Dattatawan PDP, da aka fi sani da Kwamitin Amintattu, Walid Jibrin ne ya bayyana haka.

Jibrin ya kara da cewa za a fara shirye-shiryen kafawa da rantsar da sabbin ‘yan kwamitin amintattu da zarar jam’iyyar ta cika dukkan sharuddan da dokar ta wadda aka yi wa kwaskwarima ta gindaya.

PDP ta yi wa dokar jam’iyyar kwaskwarima a taron su na ranar 9 Ga Disamba, 2017.

Cikin inda aka yi wa gyare-gayre, akwai Sashe na 8 da na 50, inda aka saukaka hanyoyin sake shiga ko dawowa jam’iyyar ga ‘ya’yan ta wadanda suka canja sheka a baya, amma kuma a yanzu su na son komawa.

An yi haka ne domin a bada rata sosai ga wanda ya dawo jam’iyyar, ta yadda zai samu sararin sake tsayawa takara a karkashin PDP, idan har ya na bukatar yin haka.

An kuma yi wa Sashe na 29, 30, 31, 35 da 45 kwaskwarima domin a samar wa jam’iyyar mataimakan shugaba na kasa guda biyu.

An yi wa Sashe na 21 kwaskwarima domin a samu damar shigar da mataimakan shugaba na kasa a ciki Kwamitin Amintattun Jama’iyya.

Baya ga wannan, akwai kuma inda aka sakala wani gyara, inda aka cusa cewa daya daga cikin mataimakan shugaba na kasa guda biyu din nan, to daya ta kasance mace, dag ya kuma namiji.

Share.

game da Author