Asusun tallafawa yara kanana na majalisar dinkin duniya (UNICEF) ta yi kira ga gwamnatocin duniya da su tsara kudirorin da za su taimaka wajen bunkasa kiwon lafiyar yara kanana a kasashen su domin samun yara masu nagarta.
UNICEF ta ce irin wadannan kudirori za su kunshi baiwa mazajen da matan su suka haihu hutu tare da biyan su albashi, baiwa matan da suka haihu hutu tare da albashi, bude makarantun da za su koyar da yara kanana kyauta a makarantu kafin su kai munzalin fara makaranta yadda ya kamata, biyan matan da suka haihu albashi saboda shayar da ‘ya’yan su nono da sauran su.
UNICEF ta ce tsarawa da kafa wadannan kudirorin zai samar wa iyaye damar kula da ‘ya’yan su wanda hakan zai taimaka wajen inganta kiwon lafiyar yara da kasan za ta alfahari da nan gaba.