Maza sun fi sauran kamuwa da cutar zuciya fiye da mata – Bincike

0

Wata farfesan cututtukan dake kama zuciya kuma ma’aikaciyar asibitin koyarwa na jami’ar Legas (LUTH) Janet Ajuluchukwu ta bayyana cewa maza sun fi kamuwa da cututtukan dake kama zuciya fiye da mata.

Ta ce ta gano haka ne a binciken da ta gudanar sannan binciken ya nuna mata cewa wannan matsalar kan kama namiji da zaran ya kai shekaru 40.

A bayanan da ta yi Janet ta ce hakan na yiwuwa ne sanadiyyar rashin zuwa asibiti a duba lafiyar su da mafi yawan maza ke kin yi.

” A yanzu haka rashin zuwa asibiti ga namiji ya zama abin yin alfahari da domin idan namiji ya yawaita zuwa asibiti sai sauran maza su yi masa kalon sakarai.”

Ta kuma ce mata kan sami kariya game da wannan matsalar domin kuwa zaka ga kusan kullum suna hanyar asibiti ne ko don su ko kuma a ‘ya’yan su daga nan sai kaga sun duba suma kansu.

Janet ta yi kira ga maza da su dinga zuwa asibiti suna duba lafiyar su domin hakan zai taimaka wa lafiyar su. Sannan suma mata su dinga taimaka wa mazajen su da tunashe su kan muhimmancin zuwa asibiti a duba su.

Share.

game da Author