Buhari ya sa hannu kan dokar takaita wa’adin mulkin Mataimakin Shugaban Kasa da na Gwamnan da suka gaji Shugaba da Gwamna

0

Shugaba Muhamamadu Buhari ya sa hannun amincewa da dokar da ta takaita wa’adin mataimakin shugaban kasa da kuma mataimakin gwamna wadanda suka karasa wa’adin shugaba ko gwamna.

A karkashin wannan sabuwar doka duk mataimakain shugaban kasa ko na gwamna da ya hau mulki ya karasa wa’adin shugaba ko na gwamna, to idan har zai yi takarar wannan mukamin, to zango daya tal kawai zai yi ba zango biyu ba.

Buhari dai ya sa wa kudirori uku hannu a ranar Juma’a wadanda a take duk suka zama doka kenan.

Sauran dokokin da ya sa wa hannu, sun jibinci harkokin zabe ne.

Babban Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara kan harkokin majalisar dattawa Ita Enag ne ya bayyana haka a ranar Juma’a.

Ya ce akwai doka wadda ta rage yawan lokacin da ake yin jekala-jekalar harkokin zabe kafin lokacin zaben da kuma kiki-kakar harkokin zabe a bayan gudanar da zaben.

Daga nan kuma sai ya kara da cewa akwai kuma kudirin da aka tura wa Buhari daga Majalisar Dattawa wanda aka sa wa hannu da ya jaddada cewa duk mataimakin shugaban kasa ko mataimakin gwamna da ya karasa wa’adin shugaba ko gwamnan sa, to idan zai tsaya takarar mukamin shugaba ko na gwamnan, sau daya kawai zai yi.


Iyanf ya ce sa wa dokar hannu ya tabbatar da cewa ba za su nemi zango na biyu ba kenan.

Ya ce wannan kudiri dai shi ne kudiri na 16.

“Tunda ya rigaya ya yi rantsuwa a matsayin gwamna ko shugaban kasa, to sau daya zai sake rike mukamin, domin rantsuwa biyu kawai ake yi a kan wadannan mukamai kamar yadda dokar Najeriya ta gindaya.”

Idan za a iya tunawa, an yi tataburza sosai a lokacin da Gooluck Jonathan ya hau mulki bayan rasuwar Umaru ‘yar Adua.

An yi ta kokarin hana shi takara zango na biyu a 2015, amma ba a yi nasara ba.

A lokacin da Jonathan ya yi nasara to za a rantsar da shi a karo na uku a kan kujerar shugaban kasa kenan.

A gyaran da aka yi wa dokar zaben maye gurbin kuwa, an maida wa’adin sake zabe zuwa kwanaki 21 maimakon kwanaki bakwai kacal.

Share.

game da Author