Gwamnatin Tarayya ta yi magana a kan zargi ko ikirarin da Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya ce, Gwamnatin Muhammadu Buhari na kokarin kitsa yadda za ta kulla masa sharrin da za a kama shi.
Obasanjo yayi wannan furuci ne a yau Juma’a, wanda gwamnatin ta yi wuf cikin hanzari ta mayar da martanin.
Obasanjo ya ce ana kokarin kitsa masa tuggu da sharrin da za a tsare shi na wani dogon lokaci, saboda ya caccaki gwamnatin Muhammadu Buhari.
A martanin da gwamnati ta dauka, Ministan Yada Labarai Lai Mohammed ya ce gwamnati ba za ta yarda a karkatar da ita wajen kitsa karya ba.
A cikin wata takarda da ya fitar ranar Juma’a, Ministan ya ce wannan gwamnatin ta na ta gaganiyar gyaran mummunar barnar da aka yi cikin shekaru 16.
A kan haka ne yace wannan gwamnatin ba ta da lokacin da za ta bata ta na goga wa wani ko wasu kashin kaji
“Ai shi mai bunu a gindi ba ya kai gudummawa kashe gobara, kuma ciki in dai ya na da gaskiya, to wuka ba ta huda shi. Sai dai shi mai gaskiya, ba zai ji tsoron bincike ba.”
“Wannan gwamnati ba za ta taba afkawa cikin kulla wa kowa sharri don a kama shi ba. Kowa ma ya san cewa wannan ba dabi’ar Shugaba Muhammadu Buhari ba ce ko ta gwamnatin sa.
“Ai wanda ba shi da mata, ba zai yi kukan mutuwa ta dauki ran surukin sa ba.
Lai ya kara da cewa kitsa tuggu da sharri bai yi kamanni ko alaka da wanan gwamnati ba. Domin a cewar sa gwamnatin Buhari ta zo ta kawar da wadannan abubuwa ne, ta shimfida adalci da sabanin mummunar surkukin dajin da aka keto a gwamnatin baya.
Discussion about this post