KIRA GA BUHARI: A dunga sara dai ana duban bakin gatari – Inji Atiku

0

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tsawata wa jami’an tsaron kasar nan kan irin fitinan da ka iya fadowa mana muddun aka ce Obasanjo za a ci wa mutunci a Najeriya.

Atiku ya ce bai kamata ace wai a yau kuma irin su Obasanjo ne za a ci wa mutunci a kasar nan ba.

Yace a dunga sara ana dubin bakin gatari kada a tado fitinan da ba za a iya kashe ta ba.

” Idan dai har ba za a yaba wa Obasanjo ba toh ko ba za a ci masa mutunci ba. Maganganun da yayi a wasikar sa ya tada min da hankali matuka cewa wai shine za a yi wa bita da kulli.

Atiku ya kara da cewa Obasanjo ya bada gudunmuwa matuka don ci gaban dimokradiyya a kasar nan sannnan ya roki shugaba Bubari da ya ja wa jami’an tsaron kasar nan kunne da su bi abin a sannu a hankali.

Share.

game da Author