Wani likitan daya kware kan gano cututtukan daji mai suna Uzodinma Kalu ya bayana cewa nan gaba matasa musamman masu shekaru 30 zuwa 50 za su fara kamuwa da cutar dajin dake kama makogwaron wuya wato ‘Thyroid cancer’ da turanci.
Kalu yace mutum kan kamu da cutar ne idan baya cin abincin dake dauke da sinadarin ‘Iodine’kamar su gishiri,kwai, ganyayyaki, madara da sauran su.
Ya kuma ce ana iya warkewa daga cutar idan an gano cutar da wuri a jikin mutum
A karshe likitan ya karyata camfin da wasu suke yi cewa wai yawan magana na kawo cutar.
Domin kauce wa kamuwa da cutar yayi kira ga matasa da su dunga cin abincin dake dauke da sinadarin ‘Iodine’
Discussion about this post