Za a fara yin fidar musanya wa mata mahaifa da na matattu don su haihu

0

Gwamnatin kasar britaniya ta ba likitocin kasar da damar yi wa matan da basu iya haihuwa fidar musanya musu wani mahaifar da na matattu domin su haifi nasu ‘ya’yan.

Idan ba a manta ba likitocin kasar sun nemi izinin gwamnati da ta basu damar ciro mahaifar macen da ta mutu domin a saka macen da nata mahaifar ya lalace.

Likitocin sun bayyana cewa hakan zai taimaka wa matan da mahaifar su ta lalace haiho nasu ‘ya’yan.

A yanzu dai gwamnatin ta amince domin a fara yin wannan fida a kasar sannan likitocin sun ce za su caji dala 66,700 farashin kudin wannan fida a kasar su.

‘‘Idan dai muka fara fidar yanzu za mu sami sakamakon aikin da muka yi a cikin shekara mai zuwa.”

Bayanai sun nuna cewa kasashen Amurka da Sweden sun fara wannan fidar inda hakan ya taimaka wa mata da dama haiho nasu ‘ya’yan a wadannan kasashe.

Share.

game da Author